Ivory Coast ta bi sahun ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, waɗanda suka kori dakarun Faransa daga cikinsu bayan sun zarge su da hannu wajen tayar da rikice-rikice./Hoto:Reuters

Sojojin Faransa za su fice daga ƙasar Ivory Coast a watan nan na Janairu, a cewar shugaban ƙasar Alassane Ouattara a wani jawabi na ƙarshen shekara da ya yi wa 'yan ƙasar ranar Talata.

Mista Ouattara ya ce ya ɗauki matakin ne da zummar zamanantar da dakarun ƙasarsa.

Ya ce, “Lokaci ya yi da za mu yi alfahari da sojojinmu, waɗanda suke aiki bisa ƙwarewa. Don haka mun yanke shawarar janye dakarun Faransa daga Cote d’Ivoire cikin lumana.”

Shugaban na Ivory Coast ya ce yanzu sojojin ƙasarsa za su maye gurbin na Faransa a Bataliya ta 43 ta Sojojin Ruwa a Port Bouet da ke kudancin Abidjan inda dakarun Faransa suka yi sansani.

Faransa tana da dakaru fiye da 600 a ƙasar Ivory Coast waɗanda ta jibge domin yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin.

Ivory Coast ta bi sahun ƙasashen Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, waɗanda suka kori dakarun Faransa daga cikinsu bayan sun zarge su da hannu wajen tayar da rikice-rikice.

Hakan na nuna yadda ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka suke ci gaba da yi mata bore, lamarin da ya rage tasirinta a nahiyar Afirka.

TRT Afrika