Hukumomin Tunisiya sun kwaso gawarwakin 'yan gudun hijira 27 da ba bisa ka'ida ba bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a gabar tekun gabashin kasar, kamar yadda wani jami'in lafiya ya bayyana.
Hatem Al-Sharif, daraktan kiwon lafiya na lardin Sfax, ya fada a ranar Alhamis cewa an ceto wasu masu neman mafaka 25 bayan da jirginsu ya nutse a gabar tekun tsibirin Kerkennah.
Ya ce kwale-kwalen na dauke ne da bakin haure daga kudu da saharar Afirka ba bisa ka'ida ba.
A ranar Litinin din da ta gabata hukumomin kasar Tunisia sun ce an gano gawarwaki biyu tare da ceto wasu 17 bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya lalace a gabar tekun arewacin kasar.
A cewar hukumar tsaron kasar, hukumomin Tunisiya sun kwaso gawarwakin bakin haure 462 tsakanin watan Janairu zuwa Mayun 2024, wanda ya ragu daga 714 a daidai wannan lokacin a shekarar 2023.
A cikin wannan lokacin, an ceto bakin haure 30,281 a shekarar 2024, yawan da ya ƙaru daga 21,652 na bara.
Yayin da ake fuskantar karuwar tashe-tashen hankula na tattalin arziki da siyasa, Tunisiya ta zama babbar hanyar wucewar bakin haure ba bisa ka'ida ba zuwa Turai.
Kusan kowane mako, hukumomin Tunisiya suna sanar da dakile yunkurin masu son wucewa masu yawa da ba a saba gani ba.
A watan Satumban shekarar 2023, Hukumar Tarayyar Turai ta yi alkawarin bayar da taimakon dala miliyan 132 ga kasar Tunisiya, a wani bangare na yarjejeniyar fahimtar juna don magance bakin haure da sauran batutuwa.