DRC President Felix

Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ya ce a shriye yake ya tattauna da takwaransa na Rwanda domin samun zaman lafiya, amma kuma ya soki wata yarjejeniya da aka ƙulla a baya-bayan nan tsakanin Rwanda da Ƙungiyar Tarayyar Turai kan haƙar ma’adinai.

“Tsokanar faɗa ce, kuma mummunan abu ne,” a cewar Shugaba Felix Tshisekedi yayin da yake magana a wajen wani taron manema labarai da aka watsa kai tsaye ta tashar talabijin ta RTNC a ranar Alhamis.

Tshisekedi ya yi zargin cewa Rwanda na kwasar albarkatun Congo. Ya soki wata yarjejeniya da aka sanya hannu a kanta tsakanin Rwanda da Tarayyar Turai a wannan makon, wacce ke da dangantaka da ƙarfafa alaƙarsu da haɗaka wajen haƙar ma’adanai, musamman ma kan muhimman ma’adanai kamar tantalum.

Ya ce bai kamata Rwanda ta ringa fitar da dukiyar da ba ta da ita ba.

Ƴan tawayen M23

Ya ƙara da cewa, da wannan yarjejeniyar mara kan gado, za su ringa samar wa sojojinsu kayan aiki, sannan su ci gaba da cimma manufarsu a Congo.

Ya zargi Rwanda da goyon bayan ƴan tawayen M23, wacce ke ƙaddamar da hare-hare a kai- a kai a gabashin Congo.

“Rwanda ta ci gaba da laɓewa a bayan M23, shi ya sa ma ba na tattaunawa da wannan ƙungiyar ta ta’addanci. Shugaban ya fadi haka ne yana mayar da martani a tambayar da a aka yi masa kan tattanawa da ƴan tawaye.

Babban abin da na sa gaba shi ne zaman lafiya, ina so a samu zaman lafiya a kasata, don haka a shirye nake in taka birki kan bukatata ta yaƙi. Idan har ba za mu iya cimma zaman lafiya ba tare da yaƙi ba zan bi wannan hanyar.

Amma idan har ta kama sai an yi yaƙi sannan za a samu zaman lafiya zan tunkare shi hannu bi-biyu,” a cewar Tshisekedi.

An tsara cewa Tshisekedi zai gana da takwaransa na Angola Joao Lourenco ranar 27 ga watan Fabrairu, a matsayin mai shiga tsakani kan rikicin.

An tsara cewa Tshisekedi zai gana da takwaransa na Angola Joao Lourenco ranar 27 ga watan Fabrairu, a matsayin mai shiga tsakani kan rikicin.

TRT Afrika