Sojojin Wagner bakwai aka kashe a Mali yayin wata arangama. Hoto/Reuters

Aƙalla sojojin hayar Rasha bakwai na Wagner aka kashe a tsakiyar Mali yayin wata arangama, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya samu waɗannan bayanan ne daga ƙungiyar nan mai zaman kanta ta SITE Intelligence wadda ke tattara bayanai dangane da abubuwan da ke faruwa na tsaro da ta'addanci a yankin.

A baya sojojin hayar na kamfanin Wagner ya rasa sojojinsa da dama a yayin wata arangama a watan Yuli da 'yan awaren Tuareg da wasu 'yan ta'adda a kusa da iyakar Mali da Aljeriya wanda hakan ya ƙara fito da irin hatsarin da sojojin na Wagner ke fuskanta a yankin na Sahel.

Mali da maƙwabtanta Nijar da Burkina Faso na ta ƙoƙarin daƙile masu ayyukan ta'addanci da 'yan aware a yankin waɗanda suka shafe fiye da shekara 12 suna tayar da zaune tsaye.

A sanarwar da SITE Intelligence ɗin ta fitar, ta bayyana cewa ƙungiyar 'yan ta'adda ta JNIM wadda ke da alaƙa da al Qaeda ce ta ɗauki nauyin kai wannan harin wanda aka kai shi a ranar Alhamis.

An ƙwace makamai

JNIM ta kashe sojojin haya na Wagner na Rasha guda bakwai tare da kwace wasu makamai, in ji SITE Intelligence.

Wani bidiyo da kamfanin dillancin labaran reuters ya gani ya nuna gawawwakin fararen fata akalla biyar sanye da kakin soji kwance a kusa da wata motar soji bayan harin da aka kai musu. Kamfanin dillancin labaran reuters ya kasa tantance sahihancin bidiyon.

Hotunan da SITE Intelligence ta yaɗa wanda aka ce daga JNIM ne ya nuna gawawwakin sojoji cikin jini da akwatunan makamai da alburusai da dama.

Ba a iya samun mai magana da yawun sojojin Mali domin jin ta bakinsa ba.

Wata majiya ɗaga ɓangaren sojojin Mali ta ce ta ga gawawwaki bakwai da suka hada da mayakan Rasha, yayin da wasu jami'an yankin biyu suka tabbatar da harin. Daya daga cikinsu ya ce an kashe mayakan Wagner biyar.

Reuters