Rundunar sojin ta wallafa wani bidiyo wanda ke nuna sojojin ƙasar a cikin hedikwatar runduna ta 17 ta sojin ƙasa da ke Sinja. / Hoto: Reuters

Rundunar Sojin Sudan a ranar Asabar ta sanar da sake kwato birnin Sinja, babban birnin jihar Sennar da ke kudu maso gabashin kasar daga hannun dakarun Rapid Support Forces (RSF).

A wata gajeruwar sanarwar da ta fitar, ta bayyana cewa “An ƙwato birnin Sinja daga hannun dakarun RSF.”

Rundunar sojin ta wallafa wani bidiyo wanda ke nuna sojojin ƙasar a cikin hedikwatar runduna ta 17 ta sojin ƙasa da ke Sinja.

Haka kuma bidiyon ya nuna yadda mazauna Sinja ke murna bayan sojojin ƙasar sun ƙwace iko da birnin na Sinja.

Zuwa yanzu dai rundunar ta RSF ba ta fitar da sanarwa dangane da lamarin ba.

A ranar 24 ga watan Yuni, RSF ta kaddamar da farmaki a jihar Sennar, inda ta kwace garuruwa da dama ciki har da Sinja, wanda suka shiga a ranar 29 ga watan Yuni.

A baya-bayan nan dai sojojin Sudan sun samu ci gaba sosai a yankin Sennar, inda suka sake kwace iko da wasu muhimman wurare kamar Jebel Moya da garuruwa kamar As-Suki da Ad-Dinder.

Tun a tsakiyar watan Afrilun bara, sojojin Sudan da RSF suka shiga cikin rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 20,000 tare da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ana ta samun kiraye-kirayen daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kasa da kasa kan a kawo karshen rikicin, yayin da yakin ya jefa miliyoyin mutanen Sudan cikin halin yunwa da rasa rayuka sakamakon karancin abinci, inda fadan ya bazu zuwa jihohi 13 daga cikin 18 na Sudan.

AA