Yadda ƙasashen Afirka da ke karkashin mulkin soja ke amfani da waƙa da al'adu don adawa da mulkin mallaka

Yadda ƙasashen Afirka da ke karkashin mulkin soja ke amfani da waƙa da al'adu don adawa da mulkin mallaka

Dubban jama'a da wakilai daga Nijar da Burkina Faso da kuma Mali ne suka halarci taron na kwanaki uku wanda aka kammala a ranar Alhamis a birnin Yamai.
Dubban mutane ne suka hallara a Yamai babban birnin Nijar domin nuna goyon bayansu ga gwamnatocin mulkin soji a yankin Sahel./ Hoto: Wasu

Dubban mutane daga ƙasashen yankin Sahel na Afirka da sojoji ke jagoranta ne suka hallara a wannan makon a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda aka gudanar da waƙe-waƙe tare da nuna al'adu domin yin Allah wadai da abin da suka kira ajandar mulkin mallaka na yammacin Turai.

Wakilai daga Nijar da Burkina Faso da Mali ne suka halarci taron na kwanaki uku wanda aka kammala a ranar Alhamis.

Shugabanin soji na ƙasashen uku na neman goyon bayan jama'a ne bayan da suka hambarar da gwamnatocin farar hula tare da yanke alaƙa da kawayensu a ƙasashen yammacin duniya wadanda suka shafe tsawon shekaru suna tare kamar Faransa, tsohuwar mulkin mallaka.

Duka ƙasashen ukun na dab da kawo ƙarshen shirin ficewarsu na shekara guda daga ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) wadda suke zargin Faransa da tunzura ta kakaba musu takunkumi saboda juyin mulkin da suka yi da kuma kasa taimakawa wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da ta kunno kai a kan iyakokinsu.

'Yan Nijar ku farka'

Wakilan da suka hallarci taron, sun hada da matasa masu goyon bayan gwamnatin mulkin sojoji da matsa da kuma ƙungiyoyin fararen hula da kuma ƙawayensu daga ko'ina a faɗin yankin Yammacin Afirka da dai sauransu inda suka mayar da hankali wajen tattauna batutuwan da suka shafi ikon ƙasashensu da kuma dangantakar tattalin arziki da tsaro da aka kulla ƙarkashin ƙungiyar ƙawance na ƙasashen uku da aka fi sani da 'Alliance of Sahel States ko AES.'

Manyan batutuwan da suka fi ɗaukar hankali su ne launuka da al'adun kasashen uku da aka zayyana a cikin kayan ado da dai sauran abubuwa da aka baje a taron da kuma wasannin kade-kade da wake-wake, wanda wani mawakin Nijar Idi Sarki ya buɗe taron da waƙarsa, wadda ta yi waiwaye kan juyin mulkin watan Yulin 2023 a ƙasar.

''Yan Nijar ku farka, ba ma son sojojin Faransa su ci gaba da zama a kasarmu,” in ji baitin waƙar da Sarki ya rera, yana mai nuni kan sojojin Faransa da aka nemi su fice daga kasar sakamakon ƙarbe iko da sojoji suka yi a Nijar da wasu ƙasashen yankin.

Mafi yawan mutanen da suka halarci taron a Yamai sun fito ne daga kasashen da sojoji ke jagoranta. /Hoto: AP

''Bayan zamanin mulkin mallaka, an ci gaba da nuna mulkin mallaka... Dole ne mu mayar da martani ko ta wacce hanya ce idan muna son iko da na tattalin arzikinmu ya- muna buƙatar albarkatun ƙasa daga yankin kudu da hamadar Sahara,'' a cewar baitin wamaƙin.

Kyakkyawan fata bayan alkawura

Kazalika wata ƙungiyar mawaƙan mata ta rera wata waƙa wadda ta sadaukar ga matasan Afirka.

Sojojin Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi alƙawarin taimaka wa wajen magance kurakuran da suka ce ya zaburar da su wajen karɓar mulki, kamar tashe-tashen hankula da matsalolin tattalin arziki da 'yan kasar ke fuskanta.

Haɗin kan Afirka

''Ta yaya za su mu rayu a ƙarkashin tsarin da ake kira dimokuradiyya, inda babu makarantu?" in ji wata tambaya da Ali Moussa wanda ya fito daga ƙasar Gabon da ke yanki tsakiyar Afirka, inda a can ma sojoji ne suke mulki. "Muna ganin cewa lokaci ya canza," in ji shi.

Akwai buƙatar a faɗaɗa gangamin yakin neman yancin kai da mulkin mallaka zuwa ƙasashen Afirka inji Inem Richardson, wacce ta fito daga Burkina Faso inda take jagorantar wani cibiyar karatu na ilimin ƙasashen Afirka mai suna Thomas Sankara Center, wani hafsan soja da ya yi juyin mulki a shekarar 1983.

''Duk 'yan Afirka na buƙatar su haɗa kai--- dole al'umma su samu abin yi,'' in ji Richardson

TRT Afrika