'Yan matan sun shafe kusan makonni biyu a hannun 'yan bindiga. Hoto/Reuters

Iyaye da 'yan uwan ‘yan matan Jami’ar Tarayya ta Gusau wadanda aka sace sun ce ba su san halin da daliban suke ciki ba tun bayan da aka sace su kusan makonni biyu da suka gabata.

Wata da ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida wa TRT Afrika Hausa cewa kanwarta na daga cikin gomman matan da aka sace daga jami’ar.

Ta bayyana cewa tun bayan da aka sace matan suka shiga tashin hankali mara misaltuwa kuma ‘yan bindigar da suka sace su ba su tuntube su ba.

“Har yanzu ba su ce komai ba, babu wanda ya kira mu, ba mu san ko suna da rai ko ba su da rai ba,” in ji ta.

Ta bayyana cewa sun yi kuka har sun gaji sakamakon rashin tabbas na halin da matan suke ciki.

A cewarta, gwamnati ba ta tuntube su ba tun bayan da aka sace daliban domin ba su wani karin bayani kan halin da ake ciki.

A kwanakin baya ne dai aka sace ‘yan mata sama da ashirin na Jami’ar Gusau da ke Jihar Zamfara duk da cewa wasu daga cikin wadanda aka sace sun kubuta.

Jama’a da dama sun harzuka tun bayan sace ‘yan matan inda ake ta tattauna batun a shafukan sada zumunta har ake zargin gwamnati da nuna halin ko-in-kula kan batun sace matan.

Sai dai gwamnatin Zamfara ta yi Allah wadai da sace matan tare da cewa suna iya kokarinsu domin ganin an ceto sauran daliban da ke hannun ‘yan bindiga bayan jami’an tsaro sun ceto wasu.

Haka kuma wasu daga cikin fitattun mutane musamman a masana’antar Kannywood sun ta daga alluna inda suke neman a saki matan.

Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin arewacin Nijeriya da ke fama da matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Ko a kwanakin baya sai da ‘yan bindigan suka sace wasu daliban a Jami’ar ta Gusau.

Haka kuma a shekarar 2021 ‘yan bindigan sun sace wasu matan na makarantar sakandare ta Jangebe kusan 300, sai dai wasu sun gudo inda daga baya aka kubutar da 279.

TRT Afrika