Batun kafa gwamnatin haɗakar na zuwa ne bayan Amurka da wasu ƙasashe sun buƙaci a tsagaita wuta a rikicin da ake yi a ƙasar. / Hoto: Reuters

Akwai yiwuwar Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Felix Tshisekedi ya kafa gwamnatin haɗaka a daidai lokacin da yake ci gaba da fuskantar matsin lamba a cikin gida dangane da yadda yake tafiyar da rikicin ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Tina Salama ce ta bayyana haka a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar.

A ranar Asabar, Shugaba Tshisekedi ya shaida wa wani taron jam’iya mai mulki kan cewa kada rikicin cikin gida ya ɗauke musu hankali: “Dole ne mu haɗa kanmu... mu haɗa kanmu domin tunkarar maƙiya.”

Tina Salama ta bayyana cewa Tshisekedi zai kafa gwamnatin haɗaka tare da gudanar da sauye-sauye a tsarin shugabanci, sai dai ba ta yi ƙarin bayani dangane da yadda sauye-sauyen za su kasance ba.

“Shugaban ƙasa ya sanar da cewa zai karkata wurin kafa gwamnatin haɗaka ta ƙasa tare da yin sauye-sauye a tsarin jagorancin sacred union,” kamar yadda ta shaida a shafinta na X.

Batun kafa gwamnatin haɗakar na zuwa ne bayan Amurka da wasu ƙasashe sun buƙaci a tsagaita wuta a rikicin da ake yi a ƙasar.

Ƙungiyar ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda na ci gaba da samun nasara a fagagen daga daban-daban a ranar.

Kungiyar a yanzu haka tana rike da yankuna da dama na gabashin DRC, yankin da ke fama da rikici. Yunkurin ci gabanta ya sa dubban mutane tserewa.

Mayakan sun kwace iko da babban birnin lardin Kivu ta Kudu Bukavu a ranar Lahadin da ta gabata, makonni bayan da suka kwace Goma, babban birnin Kivu ta Arewa kuma babban birnin da ke gabashin kasar.

A baya dai kwamitin sulhun ya yi kira da a gaggauta tsagaita buɗe wuta ba tare da wani sharadi ba, amma a ranar Juma'a dukkan kasashen da suka hada da mambobin Afirka uku sun nuna yatsa a Kigali.

TRT World