Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Botswana ya yi ajalin mutum biyar, ciki har da ƙananan yara uku, sannan ya raba dubban mutane da gidajensu, bayan an shafe kwanaki ana mamakon ruwan sama, kamar yadda Shugaban ƙasar Duma Boko ya faɗa a ranar Asabar.
Hukumomi sun rufe makarantu na ɗan wani lokaci, an kuma rufe hanyoyi bayan shafe fiye da mako guda ana ruwan sama.
“Za mu ci gaba da aiki na gajeren zango don dakatar da asarar da ake fuskanta,”a cewar Boko a wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin, yayin da aka fitar da mutane 1,700 daga yankunan da suka fuskanci ambaliyar.
A babban birnin ƙasar Gabarone, inda madatsar ruwan ke ambaliya, ruwa ya tafi da motoci sannan ya shanye kan gine-gine, yayin da ma’aikatan agaji ke cikin shiri saboda ƙarin zubar ruwan sama a kwanaki masu zuwa.
Ƙarancin magudanan ruwa
Jami’an kula da bala’o’i sun ce da alama rashin isassun magudanan ruwa a birane ne ya sa ruwan ya riƙa taruwa a wasu daga sassan da suke a kwari.
“Dole ne mu sake duba yadda muke tsara gine-ginenmu don tabbatar da cewa gine-ginenmu a matakin ƙasa za su iya jure wa fari da kuma ambaliya, a cewar Boko.