Ana yawan samun hatsarin mota a kan hanyoyin Nijeriya waɗanda da yawansu ba su da kyau. / Hoto: AA

Aƙalla muyum 14 ne hukumar da ke kiyaye hatsarin mota ta Nijeriya ta tabbatar da mutuwarsu a Jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.

Lamarin ya faru ne bayan wata mota ƙirar bas ta yi karo da wata tankar mai.

Hukumar ta FRSC ta ce bas ɗin ta afka wa tankar man ne a sakamakon direban bas ɗin yana mugun gudu sannan ya yi ƙoƙarin wuce wata bas ɗin ba bisa ƙa'ida ba a kusa da ƙauyen Kusobogi wanda ke da nisan kilomita 80 daga Minna babban birnin jihar, kamar yadda Kumar Tsukwan ya bayyana, wanda shi ne shugaban hukumar ta FRSC reshen Neja.

“Mutum 14 suka rasu sakamakon karon motocin sannan shida suka jikkata inda aka kai su asibiti domin samun ulawa,” in ji Tsukwan.

Ya ce “mugun gudu da ƙoƙarin wuce mota ba yadda ya kamata” da direban bas ɗin ya yi ne sanadin hatsarin.

Motar na hanyarta ta zuwa Kaduna ne inda ta taso daga Legas.

Ana yawan samun hatsarin mota a kan hanyoyin Nijeriya waɗanda da yawansu ba su da kyau.

A shekarar da ta gabata Nijeriya ta samu hadurran kan tituna 9,570 wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 5,421, kamar yadda bayanan hukumar FRSC suka tabbatar

TRT World