Wani babban jami'in gwamnatin Amurka, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya ce shugaban mulkin sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya amince ya tura tawaga Alƙahira ne bayan ya yi tattaunawa ta wayar tarho da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken. / Photo: AP

Gwamnatin Sudan ta ce za ta tura tawaga birnin Alƙahira domin yin tattaunawa da jami'an Amurka da na Masar ranar Litinin, a yunƙurin kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka kwashe watanni 16 ana yi a ƙasar.

Gwamnatin ƙasar, ƙarkashin sojoji da ke yaƙi da rundunar bayar da ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces (RSF) domin ƙwace iko da ƙasar, ta ce ba za ta halarci tattaunawar zaman lafiya a Switzerland ba sai an aiwatar da yarjeniyoyin da aka ƙulla a Jeddah.

Tattaunawar da Amurka ke jagoranta, wadda wakilan RSF suke halarta, tana neman kawo ƙarshen yaƙin da ya ɓarke a ƙasar a watan Afrilun 2023, tare da shawo kan bala'in rashin jinƙai da ake fama da shi a Sudan wanda ya jefa 'yan ƙasar kimanin miliyan 50 cikin tsananin yunwa.

Wata sanarwa da Majalisar Riƙon Ƙwarya ta ƙasar ta fitar ta ce ta yanke shawarar tura wakilai Alƙahira ne bayan ta tattauna da wakilin Amurka na musamman da kuma gwamnatin Masar, wadda take a matsayin 'yar-kallo a wurin tattaunawar, kuma tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla a Jeddah, inda aka amince dakarun RSF su fice daga yankunan da fararen-hula suke.

Wasu manyan jami'an gwamnati sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa gwamnati ta miƙa bayanai ga Amurka da masu shiga tsakani daga Saudiyya kan yarjejeniyar, kuma za ta ci gaba da tattaunawa ne kawai idan aka mutunta yarjejeniyar.

Jami'an sun yi fatali da rahotannin da ke cewa tuni gwamnatin Sudan ta tura wata tawaga zuwa Geneva.

Wani ƙalubale kuma shi ne, halartar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) taron, wadda gwamnatin Sudan take zrgi da goyon bayan dakarun RSF, ko da yake ta musanta zargin. Wakilan Majalisar Ɗinkin Duniya ba su ga wasu shaidu da ke nuna cewa UAE na goyon bayan RSF ba.

Gwamnatin sojin Sudan ranar Alhamis ta ce za ta ƙyale RSF ta riƙa gudanar da yankunan da ke kan iyaka zuwa Darfur domin barin masu shigar da kayan agaji zuwa ƙasar.

Wani babban jami'in gwamnatin Amurka, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya ce shugaban mulkin sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya amince ya tura tawaga Alƙahira ne bayan ya yi tattaunawa ta wayar tarho da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken.

Reuters