Hukumar da ke kula da ayyukan ‘yan sanda ta Nijeriya PSC bayar da umarni a yi ritaya ga duk wani ɗan sandn da ya haura shekara 60 da kuma wanda ya haura shekara 35 yana aikin ɗan sanda.
Hukumar ta PSC ta ɗauki wannan matakin ne a yayin wani zama na musamman da shugabanninta suka gudanar.
Zaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce game da cancantar Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya ya ci gaba da zama kan kujerarsa bayan ya cika shekara 60.
Hukumar ta PSC ta ce ta sauya shawarar da ta yanke a shekarar 2017 wadda ta amince da cewa “dole masu shiga rundunar su yi amfani da ranar da suka kama aiki maimakon ranar da aka ɗauke su aiki”, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Ikechukwu Ani ya bayyana.
“Hukumar ta sake duba hukuncin da ta yanke kuma ta yanke hukuncin cewa hukuncin da aka yanke a baya a yadda yake da manufofinsa sun saɓa wa ƙa’idar haɗewar rundunar da tsarin ma’aikatan gwamnati kuma hakan ya saɓa wa dokar ma’aikatan gwamnati mai lamba 020908 (i & ii). ) wanda ya ba da damar yin ritaya idan aka kai shekaru 35 a aiki ko kuma shekaru 60," in ji sanarwar.
“Sakamakon haka, hukumar a taronta na musamman na farko na kwamitin gudanarwa karo na 6 da aka gudanar a yau, Juma’a, 31 ga watan Janairun, 2025, ta amince da sallamar jami’an da suka shafe fiye da shekaru 35 suna aiki da wadanda suka haura shekaru 60 da haihuwa.”
Ikechukwu ya bayyana cewa tuni aka aika wa Babban Sufeton ‘Yan sandan Nijeriya Kayode Ebgbetokun da wannan hukuncin domin aiwatar da shi.