Sojojin Sudan sun samu nasarori a 'yan kwanankin nan inda suka ƙwace yankuna da dama. / Hoto: AFP

Kwamandan rundunar RSF ta Sudan Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, a ranar Juma'a ya amince da koma bayan da dakarunsa suka samu a babban birnin kasar Khartoum. 


A cikin wani faifan bidiyo da aka nada, Hemedti ya bukaci mayakansa da su mayar da hankali kan nasarorin da za su samu nan gaba, su yi watsi da yankunan da sojojin suka kwato kwanan nan. 


“Ga dukkan runduna ta kowane fanni, kada ku damu kan abin da sojoji suka kwace mana - ko babbar hedkwata (a tsakiyar Khartoum) ne, ko Signal Corps (a Bahri), garin Jili (arewacin Khartoum), ko Wad. Madani (babban birnin jihar Al-Jazira),” in ji shi. 


Ya yi kira ga dakarunsa da su mayar da hankali kan manufofinsu na gaba su yi watsi da batun yankunan da suka rasa.

Nasarorin soji

Hemedti ya yi ikirarin cewa dakarunsa za su iya sake korar sojojin na Sudan daga birnin Khartoum kamar yadda suka yi a baya.

Jawabin nasa ya zo ne bayan nasarar da sojojin Sudan suka samu a baya-bayan nan, inda suka tarwatsa kawanyar da dakarun RSF suka yi a hedkwatarsu da ke Khartoum, inda suka sake kwace iko da mafi yawan yankunan Bahri, tare da kwace Umm Ruwaba a Arewacin Kordofan. 


Tun a tsakiyar watan Afrilun 2023 ne sojoji da RSF ke fafatawa, yakin da ya kashe mutane fiye da 20,000 tare da raba kusan miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin.

Sai dai, bincike daga jami'o'in Amurka ya kiyasta adadin wadanda suka mutu ya kai kusan 130,000.

AA