Abdel Fattah al-Burhan

Shugaban rundunar sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya fita daga cikin ginin rundunar soji da ma'aikatar tsaron kasar a karon farko tun da aka soma yaki a kasar fiye da watanni hudu da suka wuce, kamar yadda wani bidiyo da rundunar ta fitar ya nuna.

Rundunar ta fitar da bidiyon ne ranar Alhamis.

Rundunar sojin da dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) sun soma gwabza fada ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata domin kwace ikon babban birnin kasar da sauran manyan birane.

Burhan - wanda ke zaune a gidan da ke cikin hedikwatar rundunar sojin kasar da ke Khartoum - ba a gan shi a bainar jama'a ba a makonni da dama.

Yunkurin da kasashen duniya suke yi domin sasanta bangarorin biyu ya ci tura inda ma'aikatan diflomasiyya suka ce kowane bangare yana ganin shi zai yi nasara.

RSF ta mamaye Khartoum da sauran biranen da ke kusa da shi yayin da rundunar sojin kasar take amfani da jiragen sama domin kawar da su daga muhimman yankunan da suka kwace.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba miliyoyi da muhallansu.

A bidiyon, wanda rundunar sojin ta ce an dauke shi a sansanin sojin sama na Wadi Sayidna da ke Omdurman, an ga sojoji suna jinjina wa Burhan.

"Ayyukan da kuke yi suna tabbatar wa jama'a cewa rundunar soji tana da sojoji kuma suna kare Sudan," in ji shi a cikin bidiyon.

Reuters