Shugaban sojojin Sudan ranar Alhamis ya gargadi Majalisar Dinkin Duniya cewa yakin da aka kwashe watanni ana yi a kasarsa zai iya watsuwa zuwa wasu kasashe a yayin da ya yi kira a matsa lamba a kan dakarun RSF da ke yaki da shi.
Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda shi ne shugaban Sudan tun bayan juyin mukin 2021, ya yi zargin cewa dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kulla kawance da kungiyar sojojin haya ta Wagner ta kasar Rasha wadda duniya ta sanya wa takunkumai saboda laifukan da take aikatawa a Afirka.
"Hatsarin wannan yakin a yanzu shi ne barazanar da yake yi ga sauran kasashe da ma duniya baki daya a yayin da wadancan 'yan tawaye suka samu goyon bayan kungiyoyin ta'addanci da aka haramta daga kasashe daban-daban na yankin da kuma duniya," in ji Burhan.
"Wannan shi ne yake ta'azzara yakin, wanda zai watsu zuwa wasu kasashe da ke yankin," in ji shi.
"A bayyane yake karar cewa wasu kasashen yankin da na duniya suna goyon bayan wadannan kungiyoyi. Hakan ne mafarin ruruwar wutar rikicin wadda za ta lakume yankin, sannan za ta yi tasiri game da yanayin tsaro da zaman lafiyar yankin da kuma na duniya."
Burhan ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana RSF a matsayin kungiyar ta'addanci, yana mai zarginta da daukar dubban sojojin haya domin yakar kasar.
A gefe guda, shugaban RSF Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya ce a shirye yake ya kawo karshen yakin kana ya rungumi zaman lumana.
A wani sakon bidiyo na ba-kasafai ba da ya yi jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya ranar Alhamis, Hemedti ya zargi tsohuwar gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir da kwace ragamar sojojin kasar.
Ya yi zargin cewa kungiyoyin masu ikirarin jihadi suna hada kai da rundunar sojin Sudan domin ganin sun dawo da tsohuwar gwamnatin.
Ranar 15 ga watan Afrilu yaki ya barke tsakanin rundunar sojin Sudan wadda Burhan yake jagoranta da dakarun Rapid Support Forces, wadanda mataimakinsa Janar Mohamed Hamdan Daglo yake shugabanta.
Yakin na Sudan ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 7,500 da kuma raba fiye da mutum miliyan biyar da muhallansu, a cewar wata kungiya mai suna Acled da ke tattara bayanai kan yakin.