Alkaluman da kungiyar Armed Conflict Location & Event Data da ke bibiyar yakin ta tattara sun ce an kasha kusan mutum 5,000 sakamakon yakin./Hoto:Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yaki da yunwa suna barazanar "durkusar" da Sudan inda dubban kananan yara masu fama da tamowa suke cikin hatsarin mutuwa, a yayin da ake ci gaba da fada tsakanin janar-janar biyu na sojin kasar.

Ta yi gargadin ne ranar Juma’a.

Yaki ya barke tsakanin shugaban rundunar sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da shugaban rundunar sa-kai ta Rapid Support Forces (RSF) Janar Mohamed Hamdan Daglo ranar 15 ga watan Afrilu.

"Yakin Sudan yana ta’azzara matsalar jinkai," a cewar Martin Griffiths, shugaban da ke kula da ayyukan agaji da na gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya.

"Wannan yakin da yake watsuwa –- da yunwa da cutuka da kuma raba mutane da muhallansu –- yanzu yana barazanar durkusar da kasar baki daya."

Alkaluman da kungiyar Armed Conflict Location & Event Data da ke bibiyar yakin ta tattara sun ce an kashe kusan mutum 5,000 sakamakon yakin.

Sai dai yakin ya hana kwaso gawarwakin wasu mutanen da suka mutu saboda barazanar fadawa cikin matsala.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan 4.6 ne yakin, wanda aka kwashe wata hudu ana yi, ya raba da muhallansu.

"Tsawon lokacin da za a kwashe ana fafatawa shi ne kuma zai tsawaita barnar da yakin ke yi. Tuni abinci ya kare a wasu wurare," in ji Griffiths a wata sanarwa da ya fitar.

AFP