Shugaban Sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan kenan yayin da yake ganawa da dakarunsa a Khartoum. / Hoto: Reuters

Shugaban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ba da sanarwar rusa rundunar dakarun sa-kai ta RSF a yammacin ranar Laraba.

Al-Burhan, wanda a yanzu shi ne shugaban majalisar mulkin kasar, ya umarci shugabannin sojojin Sudan da hukumomin kasar da su yi amfani da ikon da doka ta ba su a kundin tsarin mulkin kasar wajen rusa rundunar RSF.

Janar Al-Burhan ya dauki matakin ne "sakamakon tawayen da dakarun suka yi da ire-iren cin zarafin da suka yi wa 'yan kasar da kuma gangancin yi wa Sudan zagon-kasa".

Labari mai alaka: Wane ne Abdulfatah Al-Burhan, Shugaban Gwamnatin Soji ta Sudan?

Tun da farko dai, Amurka ta sanya wa Mohamed Hamdan Dagalo, babban jagora kuma kwamandan yankin rundunar RSF takunkumi.

Tun farkon soma gwabza yakin tsakanin dakarun RSF da Sojojin Sudan a ranar 15 ga watan Afrilu, an kashe dubban mutane tare da raba sama da mutane miliyan hudu da muhallansu, musamman a babban birnin kasar Khartoum da jihar Darfur.

TRT Afrika