Tun daga Afrilun 2023, rundunar ta RSF ke rikici da sojojin Sudan inda dubban mutane suka rasa rayukansu fiye da mutum miliyan 12 kuma suka rasa muhallansu. / Hoto: AFP

Wani ɓarin wuta da rundunar RSF ta Sudan ta yi a cikin wata kasuwa da ke birnin Omdurman ya yi sanadin mutuwar mutum 40 a ranar Asabar, kamar yadda wasu majiyoyin kiwon lafiya suka tabbatar.

Majiyar daga asibitin Al-Nao wadda ta buƙaci a ɓoye sunanta saboda tsaro ta bayyana cewa “ana ci gaba da kai waɗanda suka jikkata asibitin” bayan harin da rundunar ta RSF ta ƙaddamar.

Tun daga Afrilun 2023, rundunar ta RSF ke rikici da sojojin Sudan inda dubban mutane suka rasa rayukansu fiye da mutum miliyan 12 kuma suka rasa muhallansu.

“Ɓarin wutar ya faɗa ne a tsakayar kasuwar da ake sayar da kayan lambu, wannan ne dalilin da ya sa waɗanda suka rasu da kuma jikkata suke da yawa,” kamar yadda wani da ya tsira daga harin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wani mai aikin sa kai a asibitin Al-Nao ya shaida cewa suna cikin matuƙar buƙatar masu bayar da tallafin jini da kuma makarar da za a rinƙa ɗaukar waɗanda suka jikkata.

Asibitin na daga cikin asibitoci kaɗan da suka rage waɗanda ke aiki a yankin, inda su ma suke fuskantar hare-hare.

Bayan an shafe watanni ana kan-kan-kan tsakanin ɓangarorin biyu, a cikin watan Janairu sojojin na Sudan sun samu nasarar ƙace hedkwatarsu da rundunar ta RSF ta yi wa ƙawanya tare da samun galaba a kan RSF ta ɓangarori da dama.

AFP