Hemedti bai yi nisa a karatun boko ba inda ya bar makaranta ya kama sana'ar sayar da rakuma.

A ranar Asabar ne al'ummar duniya ta wayi gari da labarin barkewar fada tsakanin rundunar sojojin Sudan da kuma rundunar tsaro ta musamman mai suna Rapid Support Forces, RSF.

Rikici ya kaure ne bayan an kwashe tsawon lokaci ana zaman dar-dar tsakanin bangarorin biyu sakamakon yunkurin hade rundunar RSF, wadda ke da matukar karfi, a cikin rundunar sojin Sudan.

Rundunar sojin ta Sudan ta dauki matakin hade RSF a cikinta ne saboda fargabar da take yi na irin barazanar da rundunar ta musamman ke yi ga tsaron kasar.

Kafin hakan, an yi ta je-ka-ka-dawo tsakaninsu game da shirin mika mulki ga gwamnatin farar hula.

Ranar Asabar RSF ta ce dakarunta sun kwace fadar shugaban kasa da filayen jiragen sama a wani yunkuri da ake ganin tamkar na juyin mulki ne. Sai dai daga bisani rundunar sojin Sudan ta ce ita ce ke rike da ikon wadannan muhimman wurare.

Fafatawa tsakaninsu ta yi sanadin mutuwar kusan mutum 60 yayin da mutum fiye da 600 suka jikkata, ciki har da ma'aikatan Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, a cewar kungiyar likitoci ta Sudan.

Masana na ganin wannan fada ne tsakanin Abdel Fattah al-Burhan, shugaban rundunar sojin kasa kuma shugaban kasa da kuma mataimakinsa kuma shugaban RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani Hemedti.

Mece ce rundunar RSF?

An kafa RSF a 2013 karkashin jagorancin Janar Dagalo kuma ta samo asali ne daga mayakan sa-kai na Janjaweed da suka fafata da 'yan tawayen yankin Darfur.

Tun daga wancan lokacin, Janar Dagalo ya gina runduna mai matukar karfin fada a ji wadda masana suka ce tana da dakaru kusan 100,000.

Rundunar ta fafata a yake-yake da dama ciki har da na Yemen da Libya.

An zargi rundunar RSF da hannu wajen take hakkin dan adam, ciki har da kisan-gillar da aka yi wa masu zanga-zanga fiye da 120 a watan Yunin 2019.

Kawancen rundunar soji karkashin Janar Burhan da rundunar RSF da ke karkashin Dagalo ne ya kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a 2019.

Daga nan ne suka kafa gwamnati ta hadin gwiwa tsakanin farar hula da soji.

A tsarin rabon iko, Abdallah Hamdok ya zama firaiminista, yayin da Janar Burhan ke shugabancin rundunar soji kuma shugaban kasar, shi kuma Janar Dagalo ya zama mataimakinsa kuma ya cigaba da rike shugabancin rundunar RSF.

Sai dai Abdallah Hamdok ya yi murabus a watan Janairun 2022 bayan an gudanar da jerin zanga-zanga kan yadda ya raba daunin iko tsakaninsa da sojoji.

Tun daga nan komai ya koma hannun Janar Burhan da Janar Dagalo.

Masana na ganin fafatawar da ake yi a yanzu wani kokari ne na tabbatar da iko tsakanin bangarorin biyu.

A watan Disamba ne suka amince da wani shiri na mayar da mulki hannun farar hula sai dai har yanzu sun gaza kammala shirin.

Wane ne Hemedti?

An zargi rundunar RSF karkashin Hemedti da kashe farar hula fiye da 120 a 2019  ( Mahmoud Hjaj - Anadolu Agency )

An hafi Dagalo a 1974 cikin kabilar Mahariya ta kauyen Rizeigat da ke yankin Darfur.

Shafin intanet na gidan talbijin na Aljazeera ya rawaito cewa bai yi nisa a karatun boko ba, ya bar makaranta a aji uku na firamare inda daga bisani ya zama mai sayar da rakuma.

Abin da aka fi sani game da Hemedti shi ne yadda aka tilasta masa daukar makami domin fafatawa a rikicin yanki Darfur lokacin da wasu mutane suka kai hari kan tawagar 'yan kasuwar da yake jagoranta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar 'yan uwansa 60 sannan aka sace rakumansu.

Daga nan ya shiga Janjaweed, hadakar kungiyar Larabawa mayakan sa-kai da ke fafatawa a Darfur da wasu bangarori na kasar Chadi mai makwabtaka.

Ya rike mukamai daban-daban, har ya ja hankalin shugaban kasar na wancan lokaci al-Bashir, wanda ya dauki mayakan Janjaweed domin yakar mayakan sa-kai na Darfur da ke yi wa gwamnatinsa tawaye a 2003.

Ba a dade ba Dagalo ya zama kwamanda.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun zargi Janjaweed da aikata laifukan yaki, ciki har da kashe-kashe da fyade da gallaza wa fararen hula a rikicin Darfur.

TRT Afrika da abokan hulda