Jama’a da dama a shafukan sada zumunta na ta mayar da martani kan sace mata da dama da aka yi a Jami’ar Gusau.
Akasari masu rubutu a shafukan suna ta korafi inda suke cewa jama'ar arewa sun yi tsit haka zalika suna zargin gwamnati da nuna halin ko-in-kula dangane da daliban.
Sai dai a ranar Lahadi, kusan kwanaki uku kenan bayan sace daliban, Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya yi Allah wadai da sace daliban tare da cewa suna iya kokarinsu domin ganin an ceto sauran daliban da ke hannun ‘yan bindiga bayan jami’an tsaro sun ceto wasu.
Tun a ranar Juma’a shugaban Jami’ar Gusau Farfesa Mu'azu Abubakar ya tabbatar wa TRT Afrika da faruwar lamarin inda ya ce an sace daliban tun a ranar Alhamis da dare zuwa Juma’a da safe.
Baya ga daliban da aka sace, har da wasu ma’aikatan da ke gine-gine aka yi awon gaba da su.
Korafe-korafe a shafin X
Batun sace daliban na Jami’ar Gusau na daga cikin abubuwan da jama’a suka fi tattaunawa tun daga ranar Asabar musamman a shafin X wanda aka fi sani da Twitter.
A shafin X, @oil_shaeikh ya roki Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da ya yi duk mai yiwuwa wurin ceto daliban da aka sace na Jami'ar Gusau.
Haka shi ma @Waspapping_ ya roki 'yan arewa masu amfani da shafin Twitter da kada su yi kasa a gwiwa tare da cewa akwai bukatar su yi amfani da muryoyinsu har sai an saki daliban.
@AbbaM_Abiyos ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan lamarin inda yake cewa an sace dalibai mata amma arewa ta yi shiru.
Haka kuma ya kalubalanci masu fada a ji a shafukan sada zumunta da kungiyoyin arewa.
Me Kungiyar Tuntuba ta Arewa ke cewa kan wannan lamari?
Ita ma Kungiyar Tuntuba ta Arewa a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar ta yi tir da wannan lamari da kakkausar murya.
A sanarwar da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun mai magana da yawunta Farfesa T.A Muhammad-Baba, kungiyar ta jajanta wa iyayen daliban da aka sace tare da addu'ar sako daliban cikin gaggawa ba tare da lahanta su ba.
Haka kuma kungiyar ta jinjina wa jami'an tsaro kan kokarin da suka nuna duk da cewa sun 'gaza hana barayin sace daliban'.
Haka kuma kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya domin tabbatar da cewa daliban da aka sace an ceto su.