Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta mayar da martani ga wani rahoto da jaridar The Heraid ta fitar wanda ya zargi ƙungiyar da yin hasashen ɓarkewar rikici a babban zaɓen Ghana na watan Disamban 2024 da ke tafe.
ECOWAS ta yi Allah wadai da rahoton jaridar tana mai cewa Ofisoshin Jakadancin ƙungiyar ba sa fitar da ko wace irin sanarwa kan sakamakon bincike da suka gudanar gabanin zaɓukan kowace ƙasa.
A wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a shafinta na X, ta ce ''an ja hankalin ƙungiyar game da wani labari mai ban mamaki da jaridar 'The Herald' ta fitar a ranar 21 ga watan Agustan 2024, inda ta wallafa wani daftarin bayanai ɗauke da tambari da kuma turar ECOWAS na ƙarya kan sakamakon binciken da aka gudanar gabanin babban zaɓen Ghana da ke tafe tana mai zargin hukumar da hasashen ɓarkewar rikici a zaɓen Ghana na 2024.''
''Baya ga haka, ire-iren waɗannan rahotanni, na ayyukan sirri ne waɗanda shugaban hukumar ne kawai zai iya gani don su taimaka masa kan matakan da za a iya ɗauka tare da hukumomin ƙasashe mambobin ƙungiyar,'' in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ECOWAS ta ce ''har yanzu ana kan tantance ingancin rahoton farko na binciken da hukumar ta gudanar gaɓannin zaɓen Ghana, sannan babu wani lokaci ko kafin ko a yayin ko kuma bayan binciken ECOWAS da aka yi hasashen tashin hankali a cikin tsarin zaɓen.
Hukumar ta bayyana rahoton a matsayin rashin ƙwarewar aikin jaridar na The Heraid wadda ta yaɗa ƙarya a tsarin binciken ECOWAS tare da sauya al'amuran da suke a bayyane ga al'ummar Ghana.
''Hukumar ta ECOWAS tana girmama Ghana a matsayin wadda ke samun ci gaba tare da ɓunƙasa ta fuskar dimokuraɗiyya da juriya a nahiyar kuma galibi takan ba da misali da ƙasar a matsayin abar koyi a yankin,'' a cewar sanarwar.
Don haka hukumar ta yi Allah wadai da duk wani yunƙuri na wasu kafafen watsa labarai wajen amfani da sunan ƙungiyar ECOWAS ta hanyar da ba ta dace ba, a ƙoƙarinsu na haddasa fitina a tsakanin al’ummar Ghana mai mutum sama da miliyan 32 masu son zaman lafiya.
ECOWAS ta jaddada yardarta ga jajirjewar cibiyoyin dimokuraɗiyya a Ghana, kana za ta ci gaba da mara wa gwamnati da al'ummar ƙasar baya don sake gudanar da zaɓuka cikin gaskiya da adalci cikin lumana a watan Disamba na 2024.