Trump ya ba da umarnin zartarwa, kan matakan da da yawa ke da tasiri a Afirka. / Hoto: Getty Images

Donald Trump ya sanar da daukar tsauraran matakai a rana ta farko ta wa'adinsa na biyu a matsayin shugaban Amurka wanda wasu daga cikinsu za su iya shafar 'yan Afirka.

A cikin jawabinsa na rantsar da shi a ranar Litinin, kuma jim kadan bayan ya shiga Oval Office, Trump ya ba da umarnin zartarwa, kan matakan da da yawa ke da tasiri a Afirka.

Harkokin shige da fice da kora baƙin haure

A ranar Litinin ne shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da manufofinsa na shige da fice, inda ya ɗora wa sojojin Amurka aikin tsaron kan iyaka.

Da yake ayyana shige da fice ba bisa ka'ida ba a matsayin lamarin gaggawa na kasa, Trump ya umarci Ofishin Tsaro na Pentagon da ya ba da tallafi ga ginin katangar kan iyaka da wurin tsare mutane, da jigilar baƙin haure tare da bai wa sakataren tsaro ikon tura sojoji zuwa kan iyaka kamar yadda ake bukata.

Shirin da Trump ya yi na korar jama'a da ake yi wa alaƙantawa da "mugayen baƙi" mai yiyuwa ne ya shafi dubban 'yan Kudancin Amurkan da ba su da takardun zama, musamman 'yan Mexico.

Masu sharhi sun ce abin na iya shafar bakin haure 'yan Afirka da ba su da takardun shaida su ma.

A cewar Cibiyar Nazarin Hijira, an yi kiyasin cewa akwai baƙin haure 295,000 daga Afirka da ba su da izinin zama a Amurka a shekarar 2021.

Zuwa Amurka haihuwa

Donald Trump ya kuma bayar da umarnin kawo karshen abin da ake kira ba da izinin zama ‘yan kasa ga ‘ya’yan da aka haifa a Amurka wadanda iyayensu ba su da izinin shiga kasar.

Da yake ambaton dokar da aka gyara ta 14 a kundin tsarin mulkin Amurka, wani jami'in Fadar White House ya ce: "Gwamnatin tarayya ba za ta amince da 'ya'yan baki da aka haifa ba bisa ƙa'ida ba a Amurka, zama 'yan kasa na haifuwa kai tsaye. Za mu kuma inganta tsarin tantance baki."

Ga yawancin 'yan Afirka, dama hakan tuni ya zama abu mai wahala saboda tsauraran ƙa'idojin biza. Amma tun daga shekarar 2020, gwamnatin Amurka ta ƙara matsa ƙaimi.

Zai iya zama abu mai wahala ga mata 'yan kasashen waje masu ciki su je Amurka da nufin haihuwa don samun izinin zama ɗan ƙasa ga 'ya'yansu.

Manyan attajiran duniya sun halarci bikin rantsawar.

Manufofin sun bai wa jami'an ofishin jakadancin damar hana mata masu juna biyu biza ta yawon bude ido (B-2) idan sun yi imanin babban dalilin balaguron su shi ne su haihu a Amurka don samun takardar zama ɗan Amurka ga yaro.

An umurci jami’an ofishin jakadancin da su nemo alamomin da ke nuna cewa mace na iya tafiya Amurka don wani muhimmin dalili da zai sa ta je haihuwa.

Waɗannan dalilai na iya haɗawa da abubuwa kamar lokacin tafiyar (da tsohon ciki), yawan kuɗin da matafiyin ke da su da kuma tarihin tafiye-tafiyensu.

Lafiyar duniya

Trump ya rattaba hannu kan wata doka da za ta fitar da Amurka daga Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, yana mai nanata cewa ba a yi wa Washington adalci ba a ce tana biyan kudade mafu yawa da suka fi wanda China ke biya a hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.

Trump ya ce WHO ta gaza tsaywa da ƙafafunta wajen yin aiki ba tare da "tasirin siyasar da bai dace ba na kasashe mambobin WHO" kuma ta bukaci "kudaden da ba su dace ba" daga Amurka wadanda suka fi daidai yawan kudaden da wasu manyan kasashe ke bayarwa, kamar China.

"Ana zalintarmu da batun lafiyar duniya, kowa yana zalintar Amurka ta hanyar cin gajiyarta. Hakan ba zai sake faruwa ba," in ji Trump a yayin rattaba hannu kan dokar zartarwa kan janyewar, jim kadan bayan rantsar da shi a wa'adi na biyu.

Amurka ta shiga kungiyar ta WHO ta hanyar kudurin hadin gwiwa na 1948 da majalisun biyu suka zartar, kuma gwamnatocin da suka biyo baya sun goyi bayan wannan ƙuduri.

Tasiri ga Afirka

Matakin na Trump zai iya yin tasiri sosai ga Afirka, inda kawancen Amurka da WHO ya taka rawar gani wajen magance wasu kalubalen kiwon lafiyar jama'a, da suka hada da barkewar cututtuka da karancin ma'aikata, da rashin adalci a tsarin kiwon lafiya.

Amurka ta kasance babbar mai ba da gudunmawa ga WHO, tana ba da sama da dala biliyan 1.28 a tsakanin shekarar 2022-2023.

Shugaba Donald Trump ya kuma sanar da janyewar Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris,

Amurka ta kasance mai taka rawa wajen tallafa wa matakan gaggawa da WHO ke jagoranta game da barkewar cutar Ebola da cutar Marburg, da mpox.

A cikin 'yan shekarun nan, haɗin gwiwar Amurka da WHO sun taimaka wajen samar da alluran rigakafi da gina tsarin kiwon lafiya a yawancin ƙasashen Afirka.

Shirye-shiryen kiwon lafiya na dijital na WHO a Afirka, sun inganta sa ido kan rigakafi da sarrafa bayanan kiwon lafiya da tabbatar da cewa sun kai ga yawan jama'a.

Waɗannan shirye-shiryen na iya rasa ƙarfi ba tare da tallafin Amurka ba, hakan zai jefa miliyoyin yara cikin haɗarin cututtukan da za a iya rigakafin su.

Rage tallafin shirye-shiryen rigakafi na iya haifar da sake bullar cututtuka, kamar yadda wasu masana suka nuna fargaba.

Kungiyoyi kamar Afirka CDC, masu dogaro da WHO, na iya fuskantar karancin kudade, wanda zai tilasta wa kasashen Afirka daukar nauyi mai girma.

Sauyin yanayi

Shugaba Donald Trump ya kuma sanar da janyewar Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, inda ya maimaita matakin da ya dauka a wa'adinsa na farko.

Umurnin ya tsawaita ƙin amincewarTrump kan kokarin da duniya ke yi na yaki da dumamar yanayi yayin da bala'in yanayi ke kara tsananta a duniya.

Za a dauki shekara guda kafin ficewa daga yarjejeniyar bayan miƙa wata sanarwa a hukumance ga tsarin Majalisar Dinkin Duniya da ke tabbatar da shawarwarin sauyin yanayi a duniya.

Ko da yake suna ba da gudunmawa mafi kankanta ga al'amuranta, kasashen Afirka na cikin wadanda sauyin yanayi ya fi shafa.

Suna fuskantar fari da ambaliya akai-akai da sauran bala'o'i. Don haka ne suka bukaci manyan kasashen da ke gurbata muhalli, ciki har da Amurka, da su ƙara ƙaimi wajen bayar da kudaden ayyukan sauyin yanayi, yayin taron MDD kan sauyin yanayi na karshe a watan Nuwamba a Azarbaijan.

TRT Afrika da abokan hulda