Ƙungiyoyin kare muhalli na son a dakatar da malalar da wata rijiyar mai ke yi a Neja Deltan Nijeriya

Ƙungiyoyin kare muhalli na son a dakatar da malalar da wata rijiyar mai ke yi a Neja Deltan Nijeriya

Jami’ai na alakanta gobarar da wani aiki na zagon kasa da barayin mai suka yi na yunkurin satar danyen mai.
Jami’ai na alakanta gobarar da wani aiki na zagon kasa da barayin mai suka yi na yunkurin satar danyen mai. / Hoto: Reuters

An shiga mako na hudu ke nan da aka wata rijiyar mai ke malala da kuma gobarar da ta biyo baya a yankin Buguma da ke jihar Rivers a Nijeriya, ba tare da wani mataki na gaggawa da hukumomi ko jami'ai suka dauka na dakatar da barnar ba, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil'adama suka bayyana a ranar Talata.

Kungiyoyin kare muhalli (EDEN) da na Youths and Environmental Advocacy Center (YEAC-Nigeria) sun ce mazauna yankin sun sanar da su game da malalar da aka shafe makonni ana yi.

Mai magana da yawun EDEN ya ce lamarin ya zama matsalar muhalli da ta dade tana faruwa, inda ta yi kira ga hukumomi da su kashe gobarar tare da dakatar da malalar da ta haifar da gurbatar yanayi a yankin.

“Abin takaici ne cewa al’ummar yankunan da abin ya shafa sun fara wannan shekarar a mummunan yanayi tare da lalata muhallin da suke rayuwa a wajen,” in ji Chima Williams, babbar darakta a EDEN a cikin wata sanarwa.

Zagon ƙasa

Kamfanin mai na ƙasar NNPC Ltd, wanda ke kadarorin ke ƙarƙashin ikonsa, ya danganta gobarar da wani aiki na zagon kasa da barayin mai suka yi na yunkurin satar danyen mai.

Ya ce lamarin wani bangare ne na hare-haren da ake kaiwa kan rijiyoyin da ke yankin, ciki har da amfani da ababen fashewa.

Kamfanin na NNPC na ƙoƙarin daƙile gobarar kuma zai yi kokarin rage kashe kudaden da wadannan miyagun ayyuka ke jawowa, in ji kakakin.

An shafe gomman shekaru ana fama da malalar man fetur a yankin Neja-Delta a Nijeriya, lamarin da ya haifar da ɓarna mai yawa ga muhalli wanda ya lalata rayuwar miliyoyin al'ummar yankin tare da yin illa ga lafiyarsu.

Reuters