A wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin ta ce za a yi gwanajon motocin ne a ƙarƙashin wata dokarta ta 2004 da 2007 da kuma 2022.

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon ƙasa, EFCC ta sanar da shirin yin gwanjon motoci fiye da 850 da gwamnatin tarayya ta ƙwace a faɗin ƙasar.

EFCC ta ƙwato motocin ne waɗanda suka haɗa da na alfarma a binciken da take yi kan ayyukan da suka shaifi laifukan kuɗi da suka haɗa da cin hanci da halatta kudin haram da zamar intanet.

A wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na X a ranar Litinin ta ce za a yi gwanajon motocin ne a ƙarƙashin wata dokarta ta 2004 da 2007 da kuma 2022.

A cikin sanarwar, hukumar ta yi kira ga al'umma da su ci gajiyar gwanjon motocin, inda ta yi alkawarin cewa za a gudanar da tsarin cikin adalci.

Hukumar ta ce za a yi gwanjon motocin ne a Lagos da Abuja da Fatakwal da Kano, tare da hadin gwiwa da waɗanda za su sa ido don ganin yadda abin zai kaya.

EFCC ta kuma wallafa adireshin intanet din da za a iya duba motocin a sassa daban-daban, sannan ta saka ranakun da za a iya duben, wadanda suka fara daga ranar Litinin 20 ga Janairu har zuwa Litinin ta sama 27 ga Janairun 2025, tare da lokutan da za a duba din.

TRT Afrika