A yau Asabar jama’ar Jihar Ondo da ke kudancin Nijeriya suka fita zuwa rumfunan zaɓe domin zaɓen gwamnan jihar.
Zaɓen na zuwa ne watanni 11 bayan gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
‘Yan takara 18 ne hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta amince da su a matsayin ‘yan takara.
Lucky Aiyedatiwa wanda shi ne gwamnan jihar a yanzu na takarar gwamna a karon farko bayan ya maye gurbin mai gidansa Akeredolu bayan rasuwarsa.
Babban abokin takararsa na Jam’iyyar PDP wato Agboola Ajayi wanda shi ma ya taɓa yi wa Akeredolu mataimaki na daga cikin waɗanda suke fafatawa a wannan zaɓen.
Hukumar INEC ɗin ta tabbatar da cewa mutum 2,053,061 ne suke da rajista INEC ɗin ta kuma tabbatar da cewa a shirye take domin gudanar da wannan zaɓe da kuma daƙile duk wasu matsaloli waɗanda aka fuskanta a baya waɗanda suka haɗa da jigilar kayayyakin zaɓe zuwa rumfunan zaɓe.
Ita ma rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da shirinta na bayar da tsaro a yayin wannan zaɓe inda ta ce ta aika da ‘yan sanda fiye da 22,000 jihar domin tabbatar da tsaro.