Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Nijeriya ta amince da ƙudurin kasafin kudin kasar na naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025.
Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.
Wannan wani ɓangare ne na Tsarin Kuɗi na Matsakaicin-Zango da MTEF, na 2025 zuwa 2027 kuma ya yi daidai da Dokar Hada-Hadar Kuɗi (Fiscal Responsibility Act) ta 2007.
“Hakazalika, manufofin kasafin kudi sun kasance masu tsauri, saboda muna son tabbatar da cewa mun yi nazarin lamarin sosai kamar yadda muka yi imanin za a wuce abin da aka zata," a cewar Bagudu.
"Kasafin kudin da aka amince da shi don gabatar da shi ga Majalisar Dokoki ta kasa ya kai Naira Tiriliyan 47.9, tare da ciyo sabbin rancen Naira Tiriliyan 13.8 don cike gibin kasafin kudin na shekarar 2025,” in ji Bagudu.
''Muna buƙatar a daidaita yanayin kasuwa da farashin man fetur da kuma farashin musayar kuɗin ƙasashen waje, sannan a tilasta wa Kamfanin NNPCL ya rage abin da ya ke kashe wa wajen samar da man fetur da gas sosai, sannan akwai bukatar gyara wasu sassan dokar albarktun man fetur ta shekarar 2021 don shawo kan barazanar da ƙasar ke fuskanta.
“Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da tsarin kashe kuɗi na matsakaicin lokaci da kuma takardun tsare-tsaren kudin, kana za a mika su ga majalisar dokokin kasa.''
A yayin taron, FEC ta amince a miƙa wa Majalisun Dokoki na Ƙasa kudurin kamar yadda dokar da ta shafi kasafin kuɗi ta shekarar 2007 ta buƙata.
An tsara kasafin bisa hasashen samun haɓakar kayayyakin cikin gida (GDP) da kashi 4.6 cikin 100, da dora farashin mai a kan dalar Amurka 75 kowace ganga ɗaya, inda ake sa ran za a riƙa haƙar ganga miliyan 2.06 a kowace rana, da kuma ƙiyasin canjin dalar Amurka ɗaya zuwa Naira 1,400.