Shugaba Bio da dan takarar adawa Kamara sun kawo karshen yakin neman zabe a hukumance ranar Alhamis. Hoto: President Bio/Samura Kamara/Twitter

Daga Emmanuel Onyango

Miliyoyin masu zabe a kasar Saliyo ne ke shirin kada kuri'unsu don zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki a ranar Asabar.

'Yan takara 13 ne suka fito neman kujerar shugaban kasa, amma ana sa ran za a fi fafata zaben ne tsakanin shugaban kasar mai ci Julius Maada Bio na Jam'iyyar Saliyo (SLPP) da Samura Kamara na babbar jam'iyyar adawa ta All People's Congress (APC).

'Yan takarar biyu da ke kan gaba sun saba da juna wajen neman kujerar shugaban kasa, sun fafata a zabukan da suka gabata a shekarar 2018.

Jam'iyyunsu sun taba rike mulkin kasar a matakai daban-daban a lokacin juyin mulkin dimokuradiyya da kasar ta yi, sannan a bana ma ana sa ran za su kara fafatawa, a cewar manazarta.

An dai kawo karshen yakin neman zabe a hukumance a ranar Alhamis.

A shekarar 2018 ne jam’iyyar APC ta sha kaye a hannun jam’iyyar SLPP a lokacin ne aka fara zaben Shugaba Bio da ya kayar da Kamara wanda a lokacin shi ne dan takarar jam'iyyar da ke rike da mulki.

Shugaba Bio dai na fuskantar abin da masu sharhi ke cewa zaben raba gardama ne a tsawon mulkinsa na shekaru biyar. Hoto: Shafin Twitter/Shugaba Maada Bio/Twitter

Masu jefa kuri'a miliyan 3.4 aka yi wa rajista, kuma kafin a ayyana wani dan takarar a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, dole ne ya samu a kalla kashi 55% na yawan kuri’un da aka kada.

Idan babu daya daga cikin 'yan takarar da ya iya samun wannan adadi a zagayen farko, doka ta tanadi za a sake zagaye na biyu bayan mako biyu.

"Manyan jam'iyyun sun san ba za su iya cin zabe su kadai ba don haka abin da suka saba yi shi ne hada kai don samun goyon baya daga wasu tsirarun kungiyoyi don su iya samun kashi 55 cikin 100 da tsarin mulki kasa ya bukaci a samu don yin nasara," in ji Andrew Lavalie, daraktan Cibiyar sake fasalin mulki a hirarsa da TRT Afrika.

Kyakkyawan fata

Har yanzu dai kasar na kokarin farfadowa daga radadin mummunan yakin basasar da aka shafe shekara 11 ana yi wanda aka kawo karshensa kimanin shekara 20 da suka gabata.

'Yan Saliyo da dama na fatan zabukan da za a yi, wanda ke zama na biyar tun bayan kawo karshen yakin da kasar ta fi fama da shi a shekarar 2002, za su karfafa tsarin farfado da kasar tare da karfafa dimokuradiyyarta.

Batun Tattalin arziki shine babban abin da ke damun al'ummar Saliyo yayin da suke shirin kada kuri'a a ranar Asabar. Hoto: Getty

Ana kyautata zato a kan zabe a kasar, sannan akwai dumbin masu kada kuri'a a da ke hasashen hadarin hakan, a cewar manazarta.

"’Yan Saliyo suna bukatar su hada kai, su manta da dukan abubuwan da suka faru a baya tare da mai da hankali kan gaba; kuma gaban shi ne samun ci gaba mai dorewa,’’ a cewar Alhassan Fabunge, wani mazaunin babban birnin kasar, Freetown wanda TRT Afrika ta yi hira da shi.

Masu sharhi na kallon zaben a matsayin 'zaben raba gardama' kan shekara biyar da Shugaba Maada Bio ya yi yana mulki.

Tun daga kasuwanni a Freetown zuwa kan titunan da garuruwan yankin, babban abin da ke damun 'yan kasar Saliyo shi ne tattalin arziki.

'Yan hamayya sun ce tattalin arzikin kasar ya lalace da kuma tashin farashin kayayyaki da rashin ayyukan yi.

Sun gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a watan Agustan bara inda har 'yan sanda hudu da wasu masu zanga-zangar da dama suka mutu.

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa Samura Kamara, wanda tsohon ministan harkokin kasashen waje ne, ya yi alkawura, ciki har da na inganta tattalin arziki.

Samura Kamara ya yi ikirarin za a tursasa magoya bayansa a lokacin yakin neman zabe. Hoto: SamuraKamara2023/Twitter

Amma masu goyon bayan gwamnati sun ce hauhawar farashi matsala ce da duk duniya ake fuskantar ta, inda abin ya shafi kasashe da dama ba wai Saliyo kawai ba.

Sauyin dokokin zabe

Talauci ya yi tsanani inda kusan kashi 81 na 'yan Saliyo ba sa iya samun na biyan bukatu kamar cin abinci da sauran su, a bara, inda kashi 15 cikin 100 kuma suka shiga cikin tsananin talaucin da neman taimakon abinci, a cewar wani sharhi na Hukumar Abinci ta Duniya (WFP).

Amma Shugaba Bio ya ce gwamnatinsa ta yi kokari sosai wajen tafiyar da tattalin arziki "duk da halin tsananin da duniya ke fuskanta."

Ya kuma ba da misali da shirin na ba da ilimi kyauta da gwamnatinsa ta yia matsayin nasarorinsa.

A karkashin shirin, gwamnati ta ware kashi 22 cikin 100 na kasafin kudin kasar na duk shekara a cikin shekara biyar da suka gabata don bai wa yara ilimi a matakin firamare da sakandare.

Yaki da ya yi da cin hanci da rashawa ma ya sa Saliyo ta zamo ta 19 a wadanda babu cin hanci sosai a jerin kasashe 110 na duniya da hukumar da ke yaki da cin hanci ta kasa da kasa ta fitar a 2022.

Taken kamfe din shugaban kasar na tazarce shi ne "Manufofin Ci gaban Al'umma na 2023".

Shugaba Bio ya hau kan mulki ne a shekarar 2018. Hoto: Shugaba Julius Maada Bio/Twitter rike

Baya ga zabukan shugaban kasa, masu zabe za kuma su zabi 'yan majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi a ranar Asabar din.

Sakamakon zaben na iya ba da mamaki saboda ana sa ran yawan mata ya karu a majalisa, sakamakon sauyin da aka samu kwanan nan a dokokin zabe.

Ana bukatar sahihin zabe

Doka ta nemi jam'iyyun siyasa da su tabbatar a kalla kashi 30 cikin 100 na 'yan takararsu na majalisa da kananan hukumomi su kasance mata ne.

"Dole jam'iyyun siyasa su yi kokarin sanya mata a cikin jerin nan," in ji Femi Cludious,shugabar jam'iyya daya kwal da mata ke jagoranta a kasar.

A cewarta, kokarin ya dasa tambayoyi a kan cancantar wasu da aka zaba. Ba a amince da jam'iyyarta ta Cole Unity ba ana saura wata daya zaben.

Dan takarar jam'iyyar adawa Samura Kamara ya yi kira ga kwamishinonin zaben kasar da su yi murabus a kuma musanya su da wasu da kungiyoyin kasashen waje za su tantance.

Ya yi ikirari a makon da ya wuce cewa "babu wata sahihiyar rajistar masu zabe, kuma katunan zaben duk na bogi ne."

Samura Kamara ya yi alkawarin inganta tattalin arzikin kasar idan aka zabe shi. Hoto: SamuraKamara2023/Twitter

Amma shugaban hukumar zaben Mohamed Kenewui Konneh ya yi watsi da wadannan zarge-zarge yana mai cewa babu wanda zai yi murabus daga cikin tawagarsa.

Ita ma jam'iyya mai mulki ta ce hukumar zaben abar dariya ce.

Shugabannin hamayya sun kuma yi korafin cewa ana cin zarafin magoya bayansu, inda suka zargi 'yan sanda da kashe wani mutum lokacin taron da suka yi a hedikwatar jam'iyyarsu a ranar Laraba.

'Yan sanda ba su ce komai ba dangane da zargin.

'Yan kasar da dama na fatan a yi zabuka lafiya, da fatan wadanda za a zaba din za su yi aiki tukuru don inganta rayuwar 'yan kasar.

Daya daga cikin abubuwan da 'yan Saliyo ke sa rai shi ne gwamnatin da za a zaba "za ta saisaita al'amura da kuma samar wa matasa ayyukan yi, in ji Mohammed Begu, wani mazaunin birnin a hirarsa da TRT Afrika.

‘’Fatana shi ne wannan zabe ya kasance sahihi kuma marar magudi," a cewar wata 'yar kasar Justice Lamina.

TRT Afrika