Julius Maada Bio ya sake yin nasara a zaben shugaban kasar Sierra Leone

Julius Maada Bio ya sake yin nasara a zaben shugaban kasar Sierra Leone

Ya doke Samura Kamara na jam'iyyar All People’s Congress (APC), wanda ya samu kashi 41.16.
Shugaba Bio na jam'iyyar Sierra Leone People's Party (SLPP) ya samu kashi 56 na kuri'un da aka kada./Hoto: Julius Maada Bio/Facebook

Hukumar zaben Saliyo ta ayyana shugaban kasar Julius Maada Bio a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi ranar Asabar.

A sakamakon da shugaban hukumar, Mohamed Konneh, ya sanar a Freetown babban birnin kasar ranar Talata ya ce Shugaba Bio na jam'iyyar Sierra Leone People's Party (SLPP) ya samu kashi 56 na kuri'un da aka kada.

Ya doke Samura Kamara na jam'iyyar All People’s Congress (APC), wanda ya samu kashi 41.16.

Bayan sanar da kwarya-kwaryar sakamakon zaben ranar Litinin, Mr Kamara, wanda tsohon ministan harkokin wajen kasar ne, ya bayyana shi a matsayin wani "fashi da makami da aka yi da tsakar rana".

An gudanar da zaben ne cikin zaman dar-dar kuma masu sanya ido na kasashen waje sun ce an tafka kura-kurai wajen kidaya sakamakonsa.

Julius Maada Bio ya lashe zaben shugaban kasar karon farko a shekarar 2018.

TRT Afrika