Lameck Chimanikire da ke goyon bayan jam'iyya mai mulki a Zimbabwe ya ke rike da dinkin tufafin da aka yi masa don nuna goyon baya ga shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, Yuli 18, 2023./ Hoto: REUTERS/Philimon Bulawayo

Ana iya jin karar keken-dinki da ke fitowa daga shagon aiki na Judah Zunze a garin Warren Park da ke birnin Harare, yayin da yake dinka wasu tufafi na jam'iyyar siyasa ga abokin cinikinsa gabanin babban zabe da ke tafe a Zimbabwe.

Harkokin kasuwancin matashi Zunze na habaka sakamakon dinka tufafi kala-kala wadanda ke dauke da tambari da hotunan 'yan siyasa da ke takara a zaben da za a yi a Zimbabwe a ranar 23 ga watan Agusta.

Gomman 'yan takara ne suka fito neman kujerar shugaban kasa a zaben na bana, amma za a yi babbar fafatawar ce tsakanin shugaba Emmerson Mnangagwa na jam'iyyar ZANU-PF mai mulki da kuma Nelson Chamisa na sabuwar jam'iyyar CCC ta Citizens Coalition for Change (CCC).

Mnangagwa na neman wa'adi na biyu na shugabancin kasar.

"Harkokin kasuwanci na karuwa, yayin da lokacin zabe ke matsowa bukatar kayayyakin da ke dauke da tambarin jam’iyyun siyasa ta ninka a 'yan makonnin nan," a cewar Zunze, tsohon jami'in wani kamfanin tufafi.

Ya bayyana haka ne yayin da yake mika wa wani mai goyon bayan jam'iyyar ZANU-PF wasu riguna masu launin ja da baki da ya dinka masa.

Gabanin ranar zaben, masana'antun tufafin da ke zaman kansu wadanda suka hada da masu dinki irin su Zunze na samun kudade daga masu bukatar a dinka musu tufafi masu dauke da tambari jam'iyyarsu.

Zunze, wanda ya kware wajen daura aikin dinki na hoton tambarin fuskar Mnangagwa, yana cajin kudin aikinsa ne tsakanin dala 10 zuwa dala 20.

"Tun lokacin da aka fara yakin neman zabe, ina samun riba ta dala 500 a kowane wata," a cewar magidancin mai ‘yaya uku.

Ire-iren tufafin da ake dinkawa sun hada da riguna da jakunkuna da ‘yan-kwalaye a daidai lokacin da ake fama da durkushewar tattalin arzikin a kasar da kuma hauhawar farashin kayayyaki da kuma karuwar rashin aikin yi.

Ga wasu, kamar shugaban matasa na jam’iyyar ZANU-PF Lameck Chimanikire, launin tufafin masu daukar ido ba wai don a yi ado da su ba ne, don su taimaka wajen jawo hankalin matsa da kuma kuri'unsu.

Reuters