A shekarar da ta gabata ne shugaban FIFA Giovanni Infantino ya sanar da saka takunkumin kwallon kaga ga Zimbabwe. Photo: AA

Daga Takunda Mandura

Ngedwa Mpako mai shekara bakwai da aka fi sani da Mr Ronaldo kuma aka yi ta yada shi a shafukan sada zumunta na yanar gizo saboda kaunar sa ga dan kwallon kafar Portugal Cristiano Ronaldo, na mafarkin wata rana zai zama zakaran kwallon kafa a Zimbabwe, sannan ya dinga taka leda a kungiyar Manchester United.

Mr Ronaldo na daya daga cikin 'yan wasan Real Star FC, wata karamar kungiyar kwallon kafa da ke Harare wadda ke yin gwagwarmayar tsira, kuma ta dogara kan tallafi daga jama'a.

Tsawon shekaru, kwallon kafa a Zimbabwe na samun tallafi daga hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA da kuma tallafi daga daidaikun mutane.

A ranar 24 ga Fabrairu 2022, FIFA ta sanya takunkumi kan Kungiyar Kwallon Kafa ta Zimbabwe (ZIFA) daga halartar duk wata gasar kwallon kafa ta kasa da kasa saboda yadda gwamnati ke tsoma baki kan harkokin tafiyar da kungiyar.

Shugaban FIFA Giovanni Infantino ya sanar da dakatarwar a wajen taron manema labarai da aka yi ta shafin yanar gizon hukumar.

Ya ce "Dole mu dakatar da mambobinmu na Kenya da Zimbabwe, saboda yadda gwamnati ke katsalandan a harkokinsu a wadannan kasashe.

"An dakatar da kungiyoyin daga dukkan harkokin kwallon kafa. Sun san me ya kamata su yi don neman a dawo da su zuwa harkokin wasannin."

Babu nuna kwarewa

Wannan hani ya yi tasiri sosai kan harkokin kwallon kafa da 'yan wasan kasar saboda ba su da damar shiga wata gasa ta kasa da kasa.

Haramcin na FIFA ya hana Zimbabwe damar shiga gasa da wasannin kasa da kasa. Photo: TRT Afrika

Wannan mataki na haramci da FIFA ta dauka ya sake munana yanayin, inda har ta kai matakin da gwamnati ta kasa gayyatar masu zuba jari da za su habaka kayan more rayuwa na kasar.

'Yan wasan kwallon kafa na kasar ba sa samun damar nuna bajintar su ga duniya saboda ba sa bugawa kungiyar kwallon kafa ta kasar wasanni.

Wannan hani ya janyo muhawara kan makomar kwallon kafar Zimbabwe, da kuma tasirin matakin kan cigaban kwallon kafa a kasar.

Mahukuntan Zimbabwe sun bayyana suna daukar matakan ladabtarwa kan zargin cin hanci da rashin iya aiki da cin zarafin mata da ake zargin jami'an ZIFA da Felton Kamambo ke jagoranta.

Hukumar Wasanni da Nishadi ta Zimbabwe ta dauki matakin shawo kan lamarin na zargin ZIFA da ayyukan cin hanci da cin zarafin mata.

Haramcin da FIFA ta sakawa Zimbabwe ya kuma kara munana halin da ake ciki inda gwamanati ta gaza gayyatar masu zuba jari don bunkasa kayan more rayuwa a kasar.

Ayman Shraf (Hagu) da Amr Warda (Dama) na kasar Masar suke fafatawa da Tendayi Darikwa (Tsakiya) dan kasar Zimbabwe a yayin wasan bude gasar cin kofin kasashen Afirka ta 2019. Photo: AA

'Yan wasan kwallon kafa na Zimbabwe ba su samu damar buga wasanni ga kungiyar kasar ba, wanda hakan ke hana su bayyana kwarewar su ga duniya.

Wannan hani ya kuma janyo muhawara kan makomar kwallon kafa a Zimbabwe da kuma tasirin hakan ga cigaban kwallon kafar kasar..

Shugaban SRC Geral Mlotshwa a lokacin da yake mayar da martani ga FIFA kan yadda ta gaza fahimtar dokokin ZImbabwe, ya bayyana cewa "Kamar FIFA ba ta amince da dokokin Zimbabwe ba kan matakan da aka dauka game da zargin cin hanci da cin zarafin mata.

Bukatarta na dawo da wasu aiki ya zama kamar katsalandan ga dokokin SRC da kuma tsarin shari'ar kasar."

Marshall Munetsi da ke zama Zakara a Faransa ya kai maganar zuwa shafukan sada zumunta don yi roko cikin ladabi ga SRC da FIFA kan lalubo bakin zaren da zai kai ga janye wannan haramci.

Tsaftace kwallon kafa

“A lokacin da ake ci gaba da asarar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa masu hazaka saboda ba su da damar su nuna kawunansu da kwarewarsu a wasannin kasa da kasa, wannan yanayi na ci gaba da cutar da makomar kwallon kafar Zimbabwe da kuma hana al'umma amfana da kwallon kafa wadda za ta iya kawo musu cigaban zamantakewa", kamar yadda wani bangare na rubutun da ya yada ya bayyana.

Magoya bayan kwallon kafa sun damu kan hadin da FIFA ta yi wa Zimbabwe. Photo: TRT Afrika

Munetsi ya ce "Ina ci gaba da rokon SRC da ZIFA, ina kira ga dukkan bangarori da su nemo hanyar warware wannan matsala ta yadda za a samu damar kubutar da kwallon kafa a lokacin da ake kara matsawa gaba a rayuwa."

'Yan wasan cikin gida na tsoron yin magana saboda kar a kama su idan suka ce wani abu ga kafafan yada labarai.

An kuma hana ZImbabwe kudade da shirye-shiryen da za su habaka harkokin wasanninta a dukkan matakai.

Wannan hani ya janyo wa Zimbabawe asarar halartar gasa ta kasa da kasa da yawa da suka hada da na Kungiyar Wasannin Kudancin Afirka (COSAFA) da Gamayyar Tarayyar Kwallon Kafar Afirka (CAF) da wasannin sada zumunci na kasa da kasa da ma wasannin neman cancantar halartar gasar kwallon kafar Afirka ta 2023 da ta gasar Kwallon kafa ta duniya.

Kasar da ke Kudancin Afirka ta gaza halartar darussa da horar da alkalan wasa, darussan gudanarwa, likitancin wasanni, sannan sun gaza karbar kayayyaki don gudanar da harkokin wasannin.

Ministar wasanni da nishadi Kirsty Coventry wadda tsohuwar 'yar wasan ninkaya a gasar Olympic, kuma wadda ta lashe gasar kasa da kasa ta bayyana cewa ba ta son FIFA ta janyewa Zimbabwe wannan haramci a yanzu.

Babu mai laifi har sai an kama shi dumu-dumu

"Mun amince da (haramcin), ba mu taba rokar FIFA su janye shi ba, Ba ma son su janye shi a wannan gaba har sai mun tsaftace ayyukan kwallon kafa a kasarmu. Ba za mu yi abin da sauran mambobi suke fada ba", in ji ministar.

An hana Zimbabwe kudaden gudanar da harkokin wasannin kwallon kafa saboda haramcin. Photo: TRT Afrika

Hukumar ta ZIFA ta ci gaba da musanta zarge-zargen da suka janyo aka dakatar da su.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa, jami'an da aka dakatar karkashin jagorancin Felton Kamambo sun bayyana cewa "gaskiyar zance shi ne babu wani dalili da zai sanya FIFA dawo da ZImbabwe matukar matakin ba daga FIFA din ya fito ba.

"Kuma SRC ta bayyana musu hakan a boye a lokuta daban-daan. Don a sani, muna ci gaba da kasancewa 'yan kasa masu bin dokoki. kuma mun san ana ci gaba da cutar da mu ne ba bisa hakki ba."

A wata sanarwa ta hadin gwiwa kuma wadda tsaffin mambobin hukumar Philemon Machana, Bryton Malandule da tsohon Shugaba Joseph Mamutse suka sanya wa hannu, an bayyana cewa "Dokokin kasa a bayyane suke karara cewa babu mai laifi har sai an kama shi dumu-dumu, kuma muna kalubalantar duk masu zargin mu da su gabatar da shaida."

Sun kara da cewa "Ba zai yi wahala a bayyana yadda aka bai wa ZIFA dala miliyan biyu da babu su ba."

Ana ci gaba da bayyana damuwa ga aibatawa ga Hukumar Kula da Wasanni da Nishadi (SRC) yayin da magoya baya suke shirya bijirewa halartar kallon wasannin gasar PSL don bayyana rashin gamsuwarsu kan dakatar da Zimbabwe da FIFA ta yi.

"Muna son kauracewa, muna son kowa ya ga abin da ke faruwa, idan ka ga yadda muke wasanni a gasar zakaru ta kasa, ya zama kamar kwallon kan hanya ta yara.

"Ba ma matsawa ko ina, hatta alkalan wasa ba sa samun damar alkalanci a gasar kasa da kasa saboda wannan yanayi da zai kau bayan FIFA ta dawo da mu", in ji Joseph Matawu, sakatare janar na Kungiyar Masu Goyon Bayan Kwallon Kafa ta Zimbabwe.

TRT Afrika