Kungiyar Kwallon Kafa ta Al Ahly ta kasar Masar ta lashe Kofin Zakarun Turai bayan ta yi kunnen doki 1-1 da Wydad Casablanca ta Maroko a wasan karshe kuma wasa na biyu a ranar Lahadi.
Hakan na nufin Al Ahly ta yi nasara ne da ci 3-2 jimilla gida da waje kenan.
Dan wasan Wydad Yahya Attiat-Allah ne ya fara zura kwallo a minti na 27 a ragar Al Ahly, sai dai dan wasan Al Ahly Abdelmonem ya farke kwallon ana saura minti 12 a tashi wasan - abin da ya ba Al Ahly nasarar lashe kofin a karo na 11 a tarihi.
Kungiyar Wydad ta fara yin rashin nasara ne a wasan farko da suka yi a birnin Cairo na kasar Masar a farkon watan nan, da ci 2-1.
Yanzu Al Ahly ta lashe kofin gasar da ta fi shahara a Afirka sau 11 jimilla - hakan yana nufin ta kara yi wa TP Mazembe nisa wadda ita ce ta biyu a yawan lashe gasar – wadda ta lashe gasar har sau 5.
A kakar bana ne aka sake dawo da tsarin buga wasa biyu a wasan karshe - wato gida da waje kenan, bayan an yi wasan karshe a tsarin wasa daya a shekara uku da suka wuce a jere.
Wydad ce ta lashe kofin a shekarar da ta gabata bayan da ta doke Al Ahly da ci 2-0 a birnin Casablanca na Maroko.