Chelsea ta yarda ta sayi dan wasan tsakiya na Brighton and Hove Albion Moises Caicedo a kan £115m, a cewar rahotannin kafafen watsa labarai a ranar Litinin.
Bayanai sun ce ita ma Liverpool ta yi tayin sayen dan wasan mai shekara 21 dan kasar Ecuador a kan £110m ranar Juma'a.
Sai dai rahotanni a karshen mako sun ce Caicedo ya fi son tafiya Chelsea kuma zai kulla yarjejeniyar shekara takwas da kungiyar da ke yammacin London.
Chelsea, wadda ta tashi 1-1 da Liverpool a wasan farko na kakar bana a gasar Firimiya da suka fafata ranar Lahadi, tana fata Caicedo zai kasance cikin tawagar da za ta buga wasan da za su yi da West Ham United a karshen makon nan.
Mauricio Pochettino zai iya saka shi a wasa don ya yi kafada da kafada Enzo Fernandez, wanda kungiyar ta sayo daga Benfica a kan £107m a farkon shekarar da muke ciki.
Caicedo bai buga wasan farko na kakar wasa ta bana da Brighton ta doke Luton Town a gida da ci 4-1 ranar Asabar ba.