Daga Charles Mgbolu
Abu ne da ke a bayyane cewa Allah ya albarkaci Afirka da ‘yan kwallo masu basira – inda da dama daga cikinsu ke buga wa kungiyoyin kasashensu da kuma buga manyan gasanni na cikin gida da waje musamman a Turai.
Shafin bayanai na kwallon kafa na Football Benchmark ya bayar da rahoton cewa akwai ‘yan Afirka sama da 500 da ke taka leda a matakai daban-daban a Turai.
Senegal da Morocco da Nijeriya da Ivory Coast da Ghana na daga cikin manyan kasashe biyar da suka fi samar da ‘yan wasa daga Afirka a duniya.
Babu shakka an san manyan ‘yan wasan kuma ana alfahari da su.
Sai dai nahiyar na da yara kanana da matasa masu hazaka ta bangaren kwallo wadanda ke Turai.
Suna bayar da mamaki idan aka yi la’akari da shekarunsu da kuma basirarsu. Akasarinsu 'yan kasa da shekara 17 ne inda suke cike da kuzarii, da kuma fasahar kwallon kafa.
A kafafen sada zumunta, suna da dubban mabiya inda suke samun tallace-tallace ba laifi.
Ga wasu daga cikinsu daga Yammacin Afirka:
Favour Fawunmi, West Ham
Favour Fawunmi, mai shekara 16, ya shiga West Ham United Academy yana dan wasa dan kasa da shekara 15 inda ya nuna hazakarsa a abin da yake yi, kamar yadda bayanai suka nuna a shafinsa na intanet.
Fawunmi wanda bahago ne kuma dan wasan gaba, ya soma fitowa a wasa na ‘yan kasa da shekara 18 a kakar 2021/2022 inda ya saka hannu kan kwantiragi da kulob din a Yunin 2022.
Dan wasan ya haskaka a kakar, inda ya yi wasa 24 da kuma cin kwallaye goma, inda kulob din nasa ya kafa tarihi ya ci sau biyu inda ya zo daga baya ya doke Arsenal da ci 5-1 sannan ya daga kofin FA Cup na matasa a kakar 2022-2023.
A halin yanzu, West Ham ita ce a saman teburi a gasar FA ta matasa ta wannan kakar.
Cameron Okoye, FC Bescola
Shi ne dan-fari kuma da daya tal na mawakin Nijeriya nan wato Peter Okoye, wanda shi da dan uwansa ne P-Square suka yi suna a fadin nahiyar saboda wakokinsu.
Cameron, mai shekara 14, na wasa a FC Bescola wadda ita ce makarantar horarwa ta kungiyar Barcelona.
Ana yawan kwatanta shi da dan wasan gaba mai karfi a cikin sa’o’insa.
“Dana shi ne alama mafi kyau da zan bari a duniyar nan. Tauraron wasan kwallo na gobe,” kamar yadda mahaifinsa ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Kafin ya soma taka leda a FC Bescola a 2017, Cameron ya yi wasa da Little Tigers FC inda ya buga wa ‘yan kasa da shekara 9 wanda hakan ya ja aka ba shi kyautar wanda ya fi cin kwallaye a shekarar.
A watan Maris, Peter Okoye ya saka hotunan dan wasan Nijeriya da ke wasa a Napoli Victor Osimhen tare da dansa Cameron, inda yake cewa dansa na samun kwarin gwiwa daga dan wasan gaban na Napoli.
Tyron Akpata, West Ham
Tyron Akpata, mai shekara 17, dan Nijeriya ne da ya je West Ham United a matsayinsa dan wasa dan kasa da shekara 15 kafin ya saka hannu kan kwantaragi.
Matashin dan wasan tsakiyar ya ci kwallonsa ta farko daga gefe a wani wasa da aka tashi 6-0 da Norwich a Fabrairun 2023.
Ana girmama dan wasan kan irin kuzari da karsashi da ya nuna a lokacin da yake wasa na ‘yan kasa da shekara 16.
Akpata ya ji dadin kaka ta farko da bangaren su Kevin Keen a gasar ‘yan kasa da shekara 18 a West Ham, inda ya buga wasa 21, inda kungiyar ta yi nasarar cin kofin ‘yan kasa da shekara 18 na Gasar Premier League South da FA Cup Youth.
Frederick Gyan, Oxford City F.C.
Fredrick, mai shekara 15, shi ne da na farko na tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Ghana wato Asamoah Gyan.
A halin yanzu Fredrick yana buga wa Oxford City a bangaren matasa a Birtaniya.
Fredrick, wanda aka haifa a Birtaniya, ya mayar da kansa dan wasa mai kwazo bayan ya ci kofuna biyu a kakar 2020-2021 ta FA ta matasa.
Wanda ya fi ba shi kwarin gwiwa shi ne mahaifinsa da a wasu lokuta yake wallafa hotunansu a kafafen sada zumunta a lokacin da suke atisaye tare.
Kafafen watsa labarai na Ghana sun bayar da rahoton cewa Fredrick na matukar son buga wasa a matakin koli, kamar mahaifinsa, inda yake atisaye sosai a duk rana.
Taka-tsan-tsan da sha’awa
Duk da yadda amfani da kuma yadda ake son ganin matasan ‘yan wasa masu basira daga Afirka, masana na ganin a wani lokacin akwai bukatar a rinka taka-tsan-tsan dangane da yaudara da kuma zalunci wanda wasu eja-eja suke yi.
A farkon watan Yuli, tsohon dan wasan gaban Chelsea, Didier Drogba ya bayyana cewa ‘yan wasan kwallon kafa musamman a Afirka kuma matasa suna fadawa hannun eja-eja na bogi sakamakon suna musu alkawarin yin suna da kudi.
Ta hanyar gidauniyarsa, Drogba ya hada da kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta duniya FIFPRO da kuma Kungiyar Kwadago ta Duniya domin fadakarwa kan hatsarin da ke tattare da hakan.