FIFA ta dage dakatarwar da ta yi wa kungiyar kwallon kafa ta Zimbabwe (ZIFA) na tsawon watanni 18 kwanaki kadan kafin a fitar da jadawalin kasashen Afrika da suka kai ga cin gasar neman cancantar shiga wasan cin kofin duniya ta 2026.
An nada wani kwamiti na wucin gadi da zai rinka aikin duba al'amuran kungiyar ta ZIFA har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe na sabuwar tawagar gudanarwar kungiyar.
Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da kasar Zimbabwe ne a watan Fabrairun 2022 sakamakon katsalandan da gwamnati kasar ta yi a harkoki kungiyar kwallon kafar kasar wadda ta yi ta fama da rikici.
Hukumar wasanni da walwalar kasar, wadda gwamnatin Zimbabwe ta kafa ta umarci babban kwamitin gudanarwa na ZIFA da ya dakatar da ayyukuansa a watan Nuwamban 2021, bayan wani zargi da ta yi kan cewa an karkatar da wasu kudaden da aka bai wa kungiyar don halartar gasar cin kofin kasashen Afrika da ta yi a 2019.
Zimbabwe ta buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya wanda aka yi a kasar Qatar a shekarar 2022, amma an hana ta shiga wasan share fage na gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2023 da za a yi a Ivory Coast.
"Ofishin hukumar FIFA ta yanke shawarar dage dakatarwar da aka yi wa kungiyar ZIFA a watan Fabrairun 2022 tare da nada kwamitin gaggawa da zai rinka sa ido kan al’amuran kungiyar," a cewar FIFA a cikin sanarwa da ta fitar ranar Litinin.
Daga cikin ayyuka na yau da kullum da kwamitin zai mai da hankali a kai, har da yin "nazari kan dokokin ZIFA da ka'idojin zabe don tabbatar an bi ka'idoji da bukatun FIFA, da kuma tabbatar da cewa kungiyar ZIFA ta amince da su".
Lincoln Mutasa mai kula da ayyukan kungiyar ne zai jagoranci kwamitin, wanda dole ne ya kammala aikinsa a watan Yuni 2024.
Wannan sabon ci gaban da aka samu na nufin Zimbabwe za ta kasance cikin jerin kasashen da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi ranar Laraba.