Abba Kabir Yusuf ya kayar da Nasiru Gawuna a zaben watan Maris. Hoto/Abba Kabir Yusuf Facebook

Rundunar ‘yan sandan Kano da ke arewacin Nijeriya ta gargadi masu yunkurin tayar da “tarzoma” lokacin rantsar da sabon gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf da su shafa wa kansu lafiya idan ba haka ba za su dandana kudarsu.

Sanarwar da kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ranar Asabar da daddare, ta ambato Kwamishinan ‘yan sanda Mohammed Usaini Gumel yana cewa rundunarsa ta kammala “duk shirye-shiryenta kuma ta fara gudanar da sintiri na musamman don inganta tsaro ba dare ba rana a kan rantsar da sabon Gwamnan Jihar”.

Ta kara da cewa rundunar ‘yan sandan na hada gwiwa da sauran jami’an tsaro don yin amfani da karfi wajen murkushe “duk wata tarzoma da za ta iya tasowa a yayin wannan biki.”

“Don haka, ina gargadin duk masu neman haddasa fitina, da masu neman zagon kasa, da su nesanta kansu daga abubuwan da za su iya kawo tashin hankali a lokacin wannan bikin na rantsuwa,” in ji Mohammed Gumel.

A ranar Litinin za a rantsar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, a matsayin sabon gwamnan jihar ta Kano wata biyu bayan ya yi nasara a zaben da ya kayar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

Masu sharhi na ganin zaben a matsayin fafatawa tsakanin tsohon gwamnan jihar ta Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, wanda ya goyi bayan Abba, da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya mara wa Gawuna baya.

Gwamna Ganduje shi ne ya gaji Sanata Kwankwaso a 2015 sai dai tun daga wancan lokacin suka soma hamayya mai zafi ta siyasa lamarin da ya kai ga tashe-tashen hankula a lokuta da dama.

Zababben gwamnan ya gayyaci tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II domin halartar bikin rantsar da shi.

A shekarar 2020 ne Gwamna Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi na II daga kan mukaminsa bisa zargin keta dokokin aiki, zargin da tsohon sarkin ya musanta.

TRT Afrika