Gwamnan jiha ne ke da alhakin nada muhimman jami’an gwamnatin jihar da yake mulka /Hoto: Twitter

Daga Mazhun Idris

Yayin da aka yi bikin mika mulki ga sabon shugaban kasa da sabbin gwamnonin jihohin Nijeriya, masana doka da siyasa suna tsokaci kan babban kalubalen da ke gaban masu karbar madafun ikon.

Nijeriya kasa ce da ta kasu gida 37, jihohi 36 da babban birnin tarayya na Abuja.

Kasancewar akwai gwamnoni takwas da ba su kammala wa’adin mulkinsu ba, sabbin gwamnoni 28 ne za su kama aiki.

TRT Afrika ta ji ta bakin masana shari’a da siyasa kan irin hurumi da karfi da iko da dama, alfarmar da gwamnoni suke da ita a tsarin mulki da fasalin Nijeriya.

Mene ne mukamin gwamna mai cikakken iko?

Ko me ya sa ake yawan kwatanta mukamin gwamna da mukamin shugaban kasa, har ma ta kai shi ma gwamna ake masa kallon wani karamin “shugaban kasar” a jiharsa?

Lauya Mainasara Umar, masanin shari’a ne da ke birnin Abuja, kuma ya amsa wannan tambaya, inda ya sanar da TRT Afrika cewa karfin gwamna ya samo asali ne daga salon gwamnati da ake aiki da shi a tsarin mulkin Nijeriya.

“Tsarin fedaraliyya, wato tsarin tarayya da Nijeriya take kai a hukumance, ya bukaci rarraba madafun iko tsakanin gwamnatin tsakiya da ta yankuna.

“Shi ya sanya su ma gwamnonin aka ba su wasu hurumomi da alfarma don kyautata zamantakewar kasa.”

Ya kara da cewa “Gwamna mukami ne mai girma kwarai da gaske. A tsarin mulkin Nijeriya, sashe na biyu da na uku, sun ambaci matakan gwamnati guda uku, kuma gwamna shi aka sa ya shugabanci matakin jiha guda.”

Sashe na bakwai, kashi na 271 ya bayyana cewa gwamna ne ke da hurumin nada babban joji na jiha ko grand khadi, da kuma manyan alkalan babban kotun jiha, bayan samun shawara daga majalisar alkalai ta kasa.

Barista Mainasara Umar

Shi ma Dakta Aminu Hayatu, malami a Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa da ke Jami’ar Bayero ta Kano, ya fada wa TRT Afrika cewa fasalin siyasa da tsarin hukuma a Nijeriya shi ya ce akwai gwamnatin tarayya, da gwamnatocin jihohi 36, da gwamnatocin kananan hukumomi.”

Ya ce, “A kowace jiha akwai wanda ake kira gwamna, wanda ake zaba duk bayan shekara hudu. Kuma shi ke jagorantar bangaren zartarwa na jiharsa baki daya, inda yake da hurumin zartar da ayyukan gwamnati tare da taimakon mukarrabansa.”

Jerin iko da alfarmar gwamnoni lokacin mulki

Kamar yadda yake a kundin doka, a zahiri ma gwamnoni a Nijeriya suna taka muhimmiyar rawa wajen shugabantar duka harkokin gudanar da shugabanci a matakin jiha, tun daga zartar da doka ko hukunci, da kula da kudade, da nada manyan mukamai kamar sarakuna, a jihohinsu.

Ba jerin gwanon motoci da jiniya ne kadai karfin ikon gwamna ba /Hoto: Zulum Aide

Baya ga rukunan doka da tsarin mulki ya bari karkashin hurumin gwamnatin tarayya, kamar harkokin tsaron kasa, da mu’amala da kasashen waje, da iyakoki, da man fetur, da kuma shige da fice, akwai daruruwan iko da doka ta bai wa gwamna shi kadai.

Ga jerin abubuwa da suka shafi karfi da hurumin da gwamnoni suke da shi a Nijeriya.

Silken kariya daga gurfana gaban shari’a

Sabanin abin da aka sani a tsarin daidaiton al’umma, da rashin fifiko a gaban shari’a, a tsarin mulkin wasu kasashe kamar Nijeriya, ana bai wa wasu tsirarun mutane wata kariya daga gurfana gaban kotu, a yayin da suke cikin wa’adin mulki.

Gwamnonin jihohi suna sanya irin wannan silken kariya, da zarar sun sha rantsuwar kama aiki har zuwa lokacin da suka rabu da madafun iko, ba za a iya zartar da hukunci kan gwamna ba a karan-kansa, duk da dai a kan iya tilasta ita gwamnatin tasa yin wani abu.

A cewar lauya Mainasara Umar, “Sashe na 176, 177, 178, 180, musamman sadara ta shida sakin layi na biyu, sun yi bayanin karfin gwamna, da girmansa, da cancantarsa, da yadda ake zabar sa”.

A ilimi da hikima irin ta shari’a, gwamna na bukatar wannan kariya don gudun ka da tuhuma ko gurfana gaban kotu ta yi masa tarnaki a aikinsa na kula da ayyukan tsaro, da zaman lafiya, da cigaban al’ummarsa.

Nada mutane a manyan mukamai na jiha

Gwamnan jiha ne ke da alhakin nada muhimman jami’an gwamnatin jihar da yake mulka. Wannan ya kama daga sakataren gwamnatin jiha, kuma gwamnan ne ke jagorantar bikin rantsar da su kama aiki.

Gwamna ne ke zabowa kuma ya mika sunayen ‘yan majalisar zartarwarsa, wato kwamishinoni.

Akwai gwamnoni biyar da za a mayar da hankali a kansu bayan sabbin gwamnoni sun sha rantsuwa ranar 29 ga watan Mayu/Hoto:Facebook/Abba/Uba/Alex/Dauda/Alia

Bayan samun amincewar majalisar dokokin jiha, gwamna ne zai zabi ma’aikatar da zai tura kowane kwamishina. Haka nan yana da ikon cirewa ko sauyawa kowane kwamishina ma’aikatar da yake aiki.

Hakanan kuma, gwamna ne ka nada shugabannin hukumomi da cibiyoyin gwamnatin jiha, har ma da amincewa da nadin manyan sakatarorin ma’aikatu da ofisoshin gwamanatin jiha.

Yana kuma da ikon nada masu taimaka masa, da masu ba shi shawara.

Lauya Mainasara Umar ya ce, “Sashe na bakwai, kashi na 271 ya bayyana cewa gwamna ne ke da hurumin nada babban joji na jiha ko grand khadi, da kuma manyan alkalan babban kotun jiha, bayan samun shawara daga majalisar alkalai ta kasa.

Bugu da kari, gwamna ne ke da hurumin nada sarakuna masu dara ta daya zuwa ta uku, bayan ya saurari shawarar majalisar masarautun gargajiyar.

Gwamna yana da damar nada kantomomin kanana hukumomi, kasancwar yana da iko kan kananan hukomomin jiharsa.

Zartar da dokar kasa, ta majalisa jiha, da ta kotu

kasancewar gwamna mai cikakken iko ba zai tabbata sai idan an sahale masa wuka da nama, wajen aiwatar da ayyukan da doka ta tanada a matakin jiha. Gwamna shi ke jagorantar majalisar zartarwar jiha, wadda da ma shi ne ya zamo mafi rinjayen mambobinta.

Dokta Aminu Hayatu ya jaddada cewa, “Shi gwamna shi ne shugaba a bangaren zartarwa na jiah gabadaya. Duku yanke hukunce-hukunce da ba su shafi hrurumin majalisar dokoki ko na kotu ba, gwamna ne yake zartar da su.”

Ikon zartar da tsarin mulki y aba gwamna, ya kunshi ikon dabbaka duka wata doka ta tsarin mulki, ko wadda majalisar jiha ta yi, ko kuma wadda kotu ta yanke. Haka nan gwamna yana karfin kafa doka da oda daidai da karfin ofishinsa.

Hasali ma, wannan ikon zartarwa ne da gwamna yake da shi, ta sa yake nada kwamishinoni don su taya shi kula da aiwatar da kudurori da ayyukan gwamnatinsa, a lungu da sako, da kuma sassar rayuwa.

Wannan sun hada da tsaro, kudi, tattalin arziki, noma, lafiya, kasuwanci, gina kasa, muhalli, da sauransu.

Gwamna shi ke jagorantar tsara yadda za a kashe kudin jiha, inda yakan gabatar da kasafin kudin jiha a gaban majalisar jiha, baya ga cewa alhakinsa ne ya nemo dabarun samo wa jihar kudi ko dai daga haraji, zuba jari, naman tallafi, har ma da ciyo bashi.

Amma Lauya Mainasara Umar, ya kawo wani kandagarki, inda ya ce, “Kasancewar gwamna yana shugabantar matakin jiha, gwamna yana da ikon dakatar da zartarwa ko hana zartar da wata doka, matukar hakan bai zama tarnaki ga tsarin mulki ko adalci ba”.

Sai dai kuma, a yawancin jihohin Nijeriya, ba a faye zartar da hukuncin kisa ba, sakamakon gwamnoni ba kasafai suke sanya hannu kan warantin zartar da kisan kan wadanda kotu ta yanke wa hukuncin ba.

Aikin tabbatar da tsaro da bin doka da oda

Hakkin gwamna ne ya kula da zaman lafiya, rayuka, da dukiyoyin mazauna jiharsa. Alhakinsa ne magance rikici da shawo kan duk wata barazana ga zaman lumanar jiha, don tabbatar da tsaro da walwalar al’umma.

Wannan ne ya sa ake kallon n gwamna a matsayin babban jami’in tsaron jiharsa.

Lauya Mainasara Umar ya jaddawa TRT Afrika cewa, “Doka ta ba gwamna ikon amfanin da rassan hukumomin tsaro da ke jiharsa, kama daga rundunonin ‘yan sanda, da ‘yan sandan ciki, da sojoji, da sauran jami’an tsaro irin su civin defence.

Dokta Aminu Hayatu, ya ce, “Idan wani abu na tashin hankali ya faru, doka ta ayyana gwamna a matsayin babban jami’in tsaro na jiha, wanda ke jagorantar majalisar tsaron jihar mai mambobi da wakilai daga duka cibiyoyin tsaro”.

Gwamna shi ne babban jakada tsakanin gwamnatin tarayya da jama’ar jiharsa, inda yake kare hakkinsu, kamar wajen tabbatar da ‘yan jiharsa sun samu wakilci ko mukamai a gwamnatin tsakiya, da ma cibiyoyin kasa-da-kasa da ke karkashin gwamnatin tarayya.

A bangaren shari’a, doka ta bai wa gwamna alfarmar dakatar da shari’a. A cewar Lauya Mainasara, “Gwamna na da ikon zuwa kotu ya dakatar da yin wata shari’a, sakamakon ganin ana kokarin kaucewa turbar gaskiya. Gwamna zai yi haka shi da kansa ko tura wakili ko wasika”.

Gwamna yana iya yin afuwa ga daurarru, ko ya ‘yanta wadanda aka riga aka yankewa zaman gidan kaso.

Hatta wadanda aka yankewa hukunci kisa, gwamna na iya musu yafiya ko ya rage musu matakin hukuncin da ke kansu, bayan ya saurari shawarar kwamitin duba yiwuwar yafiya.

Mallaka da amfani da kasa

Ko akwai inda za a iya cewa gwamna ya fi shugaban kasa iko? Lauya Sani Garba Gwale ya tabbatar wa TRT Afrika cewa, “Idan akwai inda karfin ikon gwamna ya dara na shugaban kasa, to a dokar amfani da kasa ne”.

Lauyan ya kara da cewa, “Sashe na farko na dokar ya danka duka kasar da ke Nijeriya a hannun gwamnoni, a matsayin amana, a maimakon al’ummar Nijeriya. Gwamna shi ke da ikon mallakawa, da sanya hannu kan takardar mallakar kasa a jiharsa”.

A aikace da kuma a gwamnatance, gwamnatin tarayya tana da huruminta kan kasa, misali kasar da ta shafi albarkatun kasa, da albarkatun ruwa, da kan iyakokin kasa, da soji, da kasar da ke Abuja, da kasar da gwamnatin kasa take da takardun mallakar ta.

Sai dai kuma a cewar Lauya Sani Gwale, su ma shugabannin kananan hukumomi suna da nasu ikon kan mallakawa ko amfani da kasa, duk da cewa suna haka ne da sahalewar gwamnatin jiha.

Wanna batu na mallakar kasa shi ne ya janyo cecekuce a kwanakin baya, tsakanin gwamnoni da fadar shugaban kasa, kan barin masu dabbobi su yi kiwo a gandun dajin da ke cukin wasu jihohin Nijeriya.

TRT Afrika