Rasha ta kai kashin farko na sabbin jirage masu saukar ungulu Zimbabwe / Hoto:  Reuters

Zimbabwe ta karbi rukunin farko na jirage masu saukar ungulu daga Rasha wadanda ake sa ran za su saukaka ayyukan tsaro da na kiwon lafiya da kai daukin gaggawa a kasar.

An kai jirage 18 Zimbabwe a ranar Alhamis, jiragen dai na daga cikin jerin 32 da ake sa ran kamfanin kere-kere na Rostec da ke Rasha zai karasa kai wa kasar kafin karshen shekara mai zuwa.

"Za a yi amfani da su a amastayin jigaren sama na aikin kwana-kwana don daukar marasa lafiya da gudanar da ayyukan tsaro da kuma kai dauki cikin gaggawa a lokutan da wani bala'i ya afku", a cewar kafofin watsa labarai mallakar gwamnatin kasar.

Shugaba Emmerson Mnangagwa ya halarci bikin kai jirage masu saukar ungulun a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Harare babban birnin kasar a ranar Alhamis.

Zimbabwe ta kasance kawa ta kud da kud ga Rasha a tsawon shekaru da dama, kuma Mista Mnangagwa ya bayyana alakar da ke tsakanin kasashen biyu a matsayin "mara rabuwa, kuma wanda ya yi karkon da za a dade ana cin moriyar juna".

"A Lokacin da na tattauna da Shugaba Vladimir Putin, ya ba da shawara kan cewa kamfaninsu ya samar mana da irin kayayyakin da muke bukata, a nan ne muka ba da odar wadannan 18 din," a cewar Mista Mnangagwa.

Hakan na zuwa ne watanni hudu bayan da shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko wani makusanci ga Rasha ya kai ziyara Zimbabwe, tafiyar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce za ta taimaka wajen karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

TRT World