Akwai rahotannin jinkiri wurin soma zaben a wasu rumfuna. Hoto/TRT Afrika

Ana gudanar da zabe a kasar Saliyo inda sama da mutum miliyan uku da ke kasar ta Yammacin Afirka ke layi domin zabar shugabanninsu, ciki har da shugaban kasa.

An samu mutane sun fito daidai gwargwado a sassan kasar da suka hada da gundumomin Old Town da Bo da Kono da Karene da Pujehun.

Zuwa yanzu, rahotanni daga rumfunan zabe sun nuna cewa zaben na tafiya lami lafiya. Akwai jinkiri wurin bude kayayyakin zabe a wasu daga cikin rumfunan zabe da ke Kondebotihun a Old Town da Dwarzark da New England Ville duka da ke Freetown babban birnin kasar.

A rumfunan zabe da dama, an soma jefa kuri’a da misalin bakwai na safe a ranar Asabar. Ana rade-radin cewa zaben shugaban kasar da kuma na ‘yan majalisa zai yi zafi matuka tsakanin ‘yan takara, a daidai lokacin da ake kiraye-kirayen zaman lafiya da kuma rikicin tsadar rayuwa da ake fuskanta tun daga 2022.

Kasar Saliyo wadda ba ta farfado ba ta fannin tattalin arziki tun daga 1991 zuwa 2022 bayan yakin basasa da Annobar Ebola bayan shekara goma, da kuma annobar korona sun kara tasiri a kanta da kuma yakin Ukraine.

Zaben shugaban kasa

Maza 12 da kuma mace daya ke takarar shugabancin kasar, amma babban abokin karawar shugaba mai ci Julius Maada Bio shi ne Samura Kamara na Jam’iyyar All People’s Congress wato APC.

‘Yan takarar biyu za su sake fafatawa a karo na biyu a jere bayan Bio na Jam’iyyar Sierra Leone People’s Party SLPP ya sha da kyar a zagaye na biyu a 2018 bayan ya doke Kamara.

Batun tashin farashin kayayyakin abinci na daga cikin abubuwan da masu zabe za su fi mayar da hankali a kai a kasar mai mutum miliyan takwas da ta dogara kan shigo da kayayyaki.

TRT Afrika