Ganduje gogaggen dan siyasa ne da ya yi gwamnan Kano daga 2015 zuwa 2023./Hoto:Shafin Facebook na Abdullahi Umar Ganduje

Kwamitin zartarwa na kasa na APC mai mulkin Nijeriya ya nada tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugaban riko na jam’iyyar na kasa a ranar Alhamis.

Kazalika kwamitin ya nada tsohon kakakin majalisar dattawan kasar, Ajibola Basiru, a matsayin Sakataren Jam'iyyar na kasa.

An nada mutanen biyu ne a taron da manyan 'ya'yan jam'iyyar ta APC suka gudanar a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Da yake jawabin bayan nadin nasa, Ganduje ya gode wa Shugaban Nijeriya Bola Tinubu sannan ya yi alkawarin tabbatar da dimokuradiyyar cikin-gida a jam'iyyar ta APC.

Ya sha alwashin ganin ya sauya tsarin rajista na jam'iyyar APC zuwa na zamani wanda za a rika yi da kwamfuta.

An nada Ganduje a mukamin shugaban riko na APC ne makonni biyu bayan saukar shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu da Sakatarenta na kasa Iyiola Omisore.

Ganduje gogaggen dan siyasa ne da ya rike mukamai da dama, ciki har da gwamnan Kano daga 2015 zuwa 2023.

TRT Afrika