Salva Kiir da Riek Machar ne suka mamaye siyasar Sudan ta Kudu tun bayan da kasar ta samu ‘yanci a shekarar 2011. Hoto: OTHERS

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya yi alkawarin cewa a shekara mai zuwa za a yi zaben da aka jinkirta kuma zai tsaya takarar shugaban kasa.

Kasar ita ce ta karshe da aka kirkira a duniya kuma ta dade tana fama da rikice-rikice sannan tana karkashin mulkin hadin gwiwa tsakanin Shugaba Kiir da mataimakinsa Riek Machar.

An shirya kammala wa'adin mika mulki ne tare da gudanar da zabe a watan Fabrairun 2023, sai dai kawo yanzu gwamnati ta gaza cimma wasu muhimman tsare-tsare da suka hada da tsara kundin tsarin mulkin kasar, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.

"Na amince na tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2024," kamar yadda Kiir ya shaida wa magoya bayan jam'iyyarsa ta SPLM a ranar Talata, yayin taron da aka yi a yankin Greater Bahr El Ghazal.

Rashin amfani da lokacin da aka tsara

Ya bayyana taron da dubun dubatar mutane suka halarta a filin wasa na Wau a matsayin mai cike da tarihi.

“Mun himmatu wajen aiwatar da wani babi na cika yarjeniyoyin zaman lafiyar da muke muradi kuma za a gudanar da zabe a 2024,” in ji shi.

A watan Agusta, shugabannin biyu suka tsawaita mulkinsu na rikon kwarya da shekaru biyu, wa’adin da ya zarce lokacin da aka ware don yin zaben.

Kiir ya ce za a magance kalubalen da ake fuskanta kafin zaben.

Babu wani dan siyasa da ya bayyana aniyar tsayawa takara amma ana sa rai abokin hamayyarsa Machar zai nemi takarar.

Matsin lambar Majalisar Dinkin Duniya

Sudan ta Kudu na daga cikin kasashe mafi talauci a Afirka duk da dimbin arzikin man fetur da ta ke da shi,

Kasar ta shafe kusan rabin rayuwarta a cikin yaki. Kusan mutane 400,000 ne suka mutu a yakin basasa na shekaru biyar kafin Kiir da Machar su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a 2018 da kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Majalisar Dinkin Duniya ta sha sukar shugabannin Sudan ta Kudu kan irin rawar da suke takawa wajen tayar da tarzoma da take ‘yancin siyasa da sama-da-fadi da kudaden al’umma.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu Nicholas Haysom ya yi gargadi cikin watan Maris cewa akwai yiwuwar kasar ta iya “shudewa” a shekarar 2023, don haka dole ne shugabanninta su yi kokarin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da gudanar da sahihin zabe a 2024.

TRT Afrika