Alƙalai bakwai ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani-Abba-Aji suka yanke hukuncin inda baki ɗayansu suka yi watsi da ƙarar da aka shigar sakamakon rashin cancanta. / Hoto:  Kotun Ƙolin Nijeriya

Kotun Kolin Nijeriya ta yi watsi da wata ƙara wadda wasu jihohin Nijeriya suka shigar inda suke ƙalubalantar dokar da ta kafa hukumar EFCC.

Atoni janar na jihohi 16 ne tun da farko suka shigar da ƙarar inda suke buƙatar a soke hukumar. Sai dai wasu jihohi sun janye daga ƙarar.

Alƙalai bakwai ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Uwani-Abba-Aji suka yanke hukuncin inda baki ɗayansu suka yi watsi da ƙarar da aka shigar sakamakon rashin cancanta.

Jihohin da suka fara shigar da ƙarar sun hada da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nassarawa, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Enugu, Benue, Anambra, Plateau, Cross-River da Neja.

Sai dai kuma da a yayin da aka ci gaba da sauraren ƙarar a ranar 22 ga Oktoba, jihohin Imo da Bauchi da kuma Osun sun shiga shari’ar a matsayin masu taya shigar da ƙara, sai dai kuma Anambra da Ebonyi da Adamawa sun sanar da janyewa daga ƙarar.

An kafa hukumar EFCC ne ta hanyar dokar majalisa a ranar 12 ga watan Disambar 2002, a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Bayan kafa hukumar ta EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya zama shugabanta na farko inda hukumar ta soma aiki a ranar 13 ga Afrilun 2003.

TRT Afrika