Hukumar ta NHRC ta danganta karuwar sace-sacen mutane da kashe-kashe da kuma watsi da yara kan sakacin da ƙasar ke yi wurin kare al’ummarta. / Hoto: AA

Hukumar Kare Haƙƙin Bil’adama ta Nijeriya NHRC ta bayyana cewa mutum 1,463 ne aka kashe a ƙasar tun daga Janairun 2024 har zuwa watan Satumba.

Hukumar ta sanar da hakan ne a yayin wani taron ƙara wa juna sani da hukumar ta gudanar tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Tarayyar Turai.

Hukumar ta ƙara da cewa akwai ‘yan Nijeriya 1,172 da aka sace a ƙasar tun daga watan na Janairu har zuwa Satumba.

Baya ga alƙaluman kisa da garkuwa, hukumar ta NHRC ta kuma bayar da wasu alƙaluma waɗanda suk danganci wasu nau’ukan cin zarafi daga ciki har da watsi da yara.

“Zuwa watan Janairun 2024, mun samu alƙaluman mutm 150 waɗanda aka yi garkuwa da kuma mutum 55 waɗanda aka kashe. Abin da ya zama ruwan dare shi ne kashe jami’an tsaro,” kamar yadda wani babban jami’i a hukumar Hillary Ogbonna ya bayyana.

“Mun fara da ‘yan sanda bakwai da aka kashe a watan Janairu. Ta fuskar wadanda abin ya shafa, muna da adadi mai yawa na wadanda aka zalunta saboda take hakkin dan Adam a watan Janairu,” in ji hukumar.

Hukumar ta NHRC ta danganta karuwar sace-sacen mutane da kashe-kashe da kuma watsi da yara kan sakacin da ƙasar ke yi wurin kare al’ummarta.

TRT Afrika