Jami’an gandun daji sun yi nasarar ceto wani jaririn jakin dawa da aka dauki hotonsa yana shan nonon gawar mahaifiyarsa a yankin arewacin Kenya.
Mahaifiyar tasa ta gamu da wata matsalar lafiya ce bayan haihuwa, a cewar hukumar kula da namun daji ta Kenya.
Jaririn jakin dawan na daga cikin nau'in tsirarun jakin dawakai na Grevy, sai dai babu wata masaniya kan takamaiman lokacin da aka haife shi, amma an tura shi zuwa cibiyar ceton dabbobi.
"Wannan nasarar, ba kawai ta ceto jaririn jakin dawan ba ce, har ma da jaddada muhimmancin kiyaye namun daji da kuma ba su kariya," in ji hukumar namun daji.
An kiyasta adadin nau'in jakin dawa na Grevy da ke cikin daji sun kai kusan 2,800, kuma yawancin ana samun su ne a kudancin kasar Habasha da kuma yankin arewacin Kenya, a cewar wata gidauniyar namun daji ta Afirka.
Jariran jakin dawa kan dogara ne da uwayensu wajen samun nono har sai sun kai kimanin wata shida zuwa takwas, a cewar sakon da Gidauniyar ta wallafa a shafinta na intanet.