Shugabar IMF Kristalina Georgieva ta faɗi hakan bayan da ta ziyarci Shugaba Tinubu bayan kammala Taron Ƙungiyar G20 da aka yi a birnin Rio De Janeiro na Brazlil. Hoto: NTA

Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF, ya yaba wa gwamnatin Shugaban Nijeriya Bola Tinubu kan sauye-sauye daban-daban da aka fara yi na sake farfado da tattalin arzikin ƙasar.

Shugabar IMF Kristalina Georgieva ta faɗi hakan bayan da ta ziyarci Shugaba Tinubu bayan kammala Taron Ƙungiyar G20 da aka yi a birnin Rio De Janeiro na Brazlil.

Georgieva ta yaba wa matakan da Nijeriyar ke ɗauka waɗanda ta ce suna da nufin haɓaka tattalin arziki da samar wa 'yan ƙasar ayyukan yi.

Kalaman shugabar ta IMF suna nuni ne kan sauye-sauyen da Nijeriyar ke ci gaba da yi, wadanda suka hada da cire tallafin fetur da daidaita kudaden musaya, da manufofin maido da kwarin gwiwar masu zuba jari da karfafa tsarin kasafin kudi.

Sai dai yayin da wasu masana tattalin arziki ke ganin wadannan sauye-sauye sun zama dole, to a ɓangare guda kuma sun haifar da cece-kuce a cikin kasar, sakamakon tasirin da suke da shi kan yanayin rayuwa, yayin da ‘yan Nijeriya da dama ke fama da hauhawar farashin kayayyaki da fatara.

Shugabar ta IMF Ta bayyana cewa ganawar tata da Shugaba Tinubu ta yi "kyau sosai," inda ta fayyace ci gaban da Nijeriya ta samu a ƙoƙarinta na samun daidaiton tattalin arziki.

Saƙon da ta wallafa a shafin X ya ce, “Mun yi kyakkyawar ganawa da Shugaban Nijeriya @officialABAT a taron #G20. Na yaba wa ƙwararan matakan da Nijeriya ta ɗauka na sake fasalin tattalin arziki da haɓaka da samar da ayyukan yi ga al'ummarta. IMF tana matuƙar goyon bayan Nijeriya sosai kan wannan tafiya."

Ta ba da tabbacin cewa Asusun IMF zai ci gaba da jajircewa wajen goyon bayan Nijeriya a kan hanyartata farfaɗowa da kuma ganin ɗorewar ci gaba.

TRT Afrika