Karshen 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane a Najeriya ''ya kusa'', yayin da kasar ke samun karin kayan aikin soja daga Turkiyya, in ji Ministan Tsaron Nijeriya Mohammed Badaru Abubakar.
Minista Badaru ya yi wannan tsokaci ne a sansanin sojin saman Nijeriya da ke jihar Katsina a arewacin kasar, a lokacin kaddamar da jiragen yaki masu saukar ungulu na T129 ATAK guda biyu, wadanda kasar ta saya daga kasar Turkiyya.
“Karshen ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan daba masu dauke da makamai a kasar ya kusa,” in ji Ministan Tsaron Nijeriya a wajen taron a farkon makon nan.
Ya kuma yi kira ga rundunar sojin sama da ta hada kai da sojojin kasa da sauran masu ruwa da tsaki domin samun nasara a kan makiya kasar.
Karin jirage masu saukar ungulu na T129 ATAK guda biyu da aka kai a watan Satumba sun karfafa yaki da kungiyoyi masu dauke da makamai, in ji ministan.
Haɓaka alaƙa
Mista Abubakar ya bukaci jami’an tsaro da su ƙara zage damtse wajen ganin sun kawar da ‘yan ta’adda masu dauke da makamai, da kuma kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISWAP, yana mai jaddada cewa suna barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da walwala.
Nijeriya ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin ƙera jiragen yaƙi na Turkiyya, TAI, na sayen jirage masu saukar ungulu na T-129 ATAK guda shida domin bunkasa karfin sojojinta na sama.
Kasar ta Afirka ta Yamma ta samu biyu daga cikin jirage masu saukar ungulu na yaki a watan Fabrairu, biyu kuma a watan Satumba, yayin da ake kan aikin ƙera sauran biyun.
Jirgin yaki na T-129 ATAK da TAI ta ƙera na daga cikin kayan aikin soja da Turkiyya ta ƙera da ke jan hankalin duniya.
Dangantakar soji da tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Turkiyya na ci gaba da bunkasa.
A cikin 'yan shekarun nan, kasashen biyu sun samu ci gaba sosai, kuma ana sa ran za su rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar tsaro ta sama da dala biliyan biyu nan gaba, a cewar majiyoyin.
Jami'an Nijeriya karkashin jagorancin Ministan Tsaro sun ziyarci Turkiyya a watan Fabrairun wannan shekara inda suka tattauna da sakataren masana'antun tsaro na fadar shugaban kasar ta Jamhuriyar Turkiyya Farfesa Dr Haluk Görgün.