Abdoulaye Maiga ya yi jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a hedkwatar Majalisar da ke birnin New York. Hoto/Reuters  

Gwamnatin mulkin sojin a Mali ta nada janar Abdoulaye Maiga a matsayin sabon firaminista ƙasar a ranar Alhamis, bayan da ta kori ministan farar hula Choguel Kokalla Maiga kwana ɗaya da sukar da ya yi wa shugabannin sojojin ƙasar.

''An nada Manjo Janar Abdoulaye Maiga Firaiminista,'' a cewar wata sanarwa da shugaban mulkin sojin ƙasar ya fitar, Janar Assimi Goita ya fitar, wanda babban sakataren fadar shugaban kasa ya karanta ta gidan talabijin ɗin gwamnati ƙasar ORTM.

Maiga a ranar Asabar ɗin da ta gabata ya yi kira ga sojojin ƙasar su kawo ƙarshen riƙon ƙwaryar da suke yi a ƙasar.

"Ya kamata gwamnatin riƙon ƙwarya ta zo ƙarshe a ranar 26 ga watan Maris ɗin 2024. Sai dai an ɗage yin hakan har illa masha Allahu, ba tare da muhawara da ɓangaren gwamnati ba," kamar yadda Maiga ya shaida wa magoya bayan tafiyar M5-RFP a wani jawabi da ya gabatar.

Ƙasar na ƙarƙashin jagorancin sojoji tun bayan jerin juyin mulkin da aka gudanar a ƙasar a shekarun 2020 da kuma 2021.

A watan Yunin 2022, gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta yi alƙwarin gudanar da zaɓe da kuma miƙa mulki ga farar hula zuwa ƙarshen watan Maris ɗin 2024, sai dai an ɗage yin hakan.

Tun daga shekarar 2012, Mali na fama da rikicin siyasa da tsaro, wanda rikicin 'yan ta'adda masu riƙe da makamai da 'yan tawaye suka ta'azzara.

AA

TRT Afrika