Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya yi maraba da 'yan asalin Afirka 524 da ƙasar ta bai wa shaidar zama ɗan ƙasa.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce shugaban ya buƙace su da su haɗa kai su ba da gudunmawarsu ga ci-gaban ƙasar.
Sabbin 'yan ƙasar Ghanan sun sha rantsuwar zama 'yan ƙasar ne a yayin wani biki da aka gudanar, wanda hakan wani ɓangare ne na shirin dawowa da baƙaken-fata da aka ɗauke daga Afirka a lokacin cinikin bayi.
An ƙaddamar da shirin ne a cikin shekarar 2019, shekara 400 bayan an fara kai 'yan Afirka Amurka a matsayin bayi.
Shirin na son ƙara haɗa kan Ghana da tarihinta da kuma ƙara danƙon zumunci tsakaninta da 'yan asalin Afirka da ke ƙasashen ƙetare, in ji sanarwar.
A jawabinsa Shugaban Akufo-Addo ya jaddada muhimmancin haɗin-kai da haƙuri da kuma manufofi iri ɗaya.
Miliyoyin 'yan Afirka ne dai aka kai nahiyar Amurka a matsayin bayi a lokacin cinikin bayi.