Jami’an kashe gobara sun kubutar da sama da mutane 40, inda mazauna yankin suka ringa kai ɗauki don fitar da waɗanda suka maƙale.
Wasu da lamarin ya rutsa da su ‘yan ƙasashen waje ne waɗanda suka je Indiya don neman lafiya. Har yanzu ana ci gaba da binciken musabbabin gobarar.
