| Hausa
Jiragen ruwan Iran masu gudun tsiya na tsintiri a mashigar Hormuz, in ji gidan talabjin din gwamnati
00:28
Jiragen ruwan Iran masu gudun tsiya na tsintiri a mashigar Hormuz, in ji gidan talabjin din gwamnati
Gidan talabijin ɗin Iran ya watsa bidiyon da ya ce yana nuna jiragen ruwa masu gudun tsiya na Rundunar Kare Juyin Jjuya-Halin ƙasar suna sintiri a mashigar ruwan Hormuz.

Gidan talabijin ɗin ya ƙara da cewa manufar sintirin shi ne raka jiragen ruwa masu wucewa da kuma hana duk wani jirgin ruwan da ya ƙeta gargaɗin rundunar.

Kafafan watsa labaran Iran sun bayyana a ranar Talata cewa a yanzu an buɗe tsarin neman izinin wucewar jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz, abin da zai ba da dama ga masu jiragen ruwa da jagororin jiragen ruwa a fadin duniya su nemi izinin wucewa a kowane lokaci .

A ranar kuma, sojin ruwa na rundunar IRGC sun ce jiragen ruwa 24 sun wuce ta mashigar ruwan Hormuz cikin sa’o’i 24 da haɗin gwiwardakarunta.

Jiragen ruwan sun wuce ta hanyar ruwan ne a ƙarƙashin kariyar dakarun sojin ruwan rundunar IRGC bayan sun sami izini, in ji ɓangaren hulɗa da jama’a na sojin ruwa na rundunar IRGC.

Ƙarin Bidiyoyi
Shugaba Erdogan ya karbi bakuncin Tiani na Nijar a birnin Ankara na Turkiyya
Jam'iyyun siyasa da 'yantakararsu a zaben shugaban kasa na 2027
Gobarar New Delhi ta halaka mutum 21
Ojude Oba: Bikin al'adar gargajiya da ake gudanarwa bayan babbar Sallah
''Dole mu kashe tunanin za a iya samar da kasar Falasdinawa''
Sabon shugaban kasar Benin ya kai ziyara Nijar
Iran ta sanar da 'harin ramuwar gayya' a tekun Oman
Isra'ila ta kai hare-hare da dama a kusa da asibitin Jabal Amel a Lebanon
Batun satar dalibai da malamai a jihar Oyon Nijeriya
Mutum-mutumi da jirage marasa matuka sun kayatar da 'yan kallo