| Hausa
Iran ta sanar da 'harin ramuwar gayya' a tekun Oman
00:31
Iran ta sanar da 'harin ramuwar gayya' a tekun Oman
A ranar Litini Iran ta dakatar da tattaunawa kai-tsaye da aika rubutattuna saƙonni tsakaninta da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, don nuna rashin jin daɗi kan yadda Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Lebanon.

Rundunar Kare Juyin Juya-Hali ta Iran (IRGC) ta ce dakarun sojin ruwanta sun kai hari kan wani jirgin ruwa mai suna MSC Sariska da makami mai linzami a wani abin da ta bayyana a matsayin wani "aikin ramuwar gayya" biyo bayan wani abin da ta kira harin Amurka a kan wani jirgin ruwan Iran a tekun Oman.

Wata sanarwa da kafar watsa labaran ƙasar Iran IRIB ta samu ranar Litinin ta ce harin ya zo ne bayan abin da IRGC ta kira wani "hari na tsokana" da sojin Amurka ta kai kan wani jirgin ruwan Iran mai suna Lian Star a tekun Oman.

Sanarwar ta yi iƙirarin cewa jirgin mai suna MSC Sariska mallakin abin da ta kira "abokan gaba Amurka da masu kaifin kishin kafa ƙasar Yahudawa."

Jami'an Iraƙi sun ce an kai wa jirgin hari da abubuwna fashewa biyu, rahotanni sun ce ɗaya daga cikinsu jirgi mara matuƙi ne ya kai masa hari.

Ƙarin Bidiyoyi
Isra'ila ta kai hare-hare da dama a kusa da asibitin Jabal Amel a Lebanon
Batun satar dalibai da malamai a jihar Oyon Nijeriya
Mutum-mutumi da jirage marasa matuka sun kayatar da 'yan kallo
Makon Abincin Turkiyya: Yadda na girka Kuru Fusulye
Alhazai sun hau Dutsen Arfa
Yadda aka ayyana Pantami a dantakarar gwamnan Gombe a PDP
Ethnosport: Ana bikin wasannin gargajiya na duniya a Istanbul
Kasashe 50 sun shiga atisayen sojin Turkiyya na Fees - 2026
Yadda wata babbar mota ta kwace ta yi ajalin mutum hudu a Gombe
'Yansandan New York sun kama mutumin da ya yi wa Musulmai barazana da wuka